Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 14.10.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 14.10.2019

72
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, goma sha biyar ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha hudu ga Oktoban 2019.

  1. Aisha Buhari ta dawo daga Ingila bayan dogon hutu da ta sha, ta kuma ce bidiyon da aka nuna tana fada a fadar shugaban kasa, ita ce amma tsohon faifai ne. Ta kuma bayyana wa BBC Hausa cewa masu yada labarin ta yi yaji ga mijinta zai yi aure, ita ba ta ma san mene ne yaji ba. Ta ce wadanda ke ta nuna gawa suna cewa Buhari ne ya mutu a lokacin da ya yi jinya, to su ne suka kitsa labarin ta yi yaji kuma an sansu aka kyale suka ci gaba da yi.
    Ta ce ita ta je hutu ne da ‘ya’yanta kuma ta saba zuwa wannan hutu ba wai yaji ta yi ba.
  2. Sojoji sun kashe ‘yan bindiga su talatin da tara, da wani shugabansu cikon na arba’in a jihar Zamfara, suka kuma tarwatsa tungarsu daban-daban har uku.
  3. Kungiyar kwadago ta NLC ta umarci ma’aikata su kasance cikin shirin bazama yajin aiki jibi laraba, idan gwamnati ta ci gaba da yi wa kungiyar kwaneri a kan sabon albashi.
  4. PDP ta yi zargin gwamnatin APC na shirin yi wa ‘yancin fadin albarkacin baki da kafofin yada/watsa labaru suke da shi hawan kawara.
  5. APC ta ce rashin kwakkwarar adawa daga PDP ya sa kasar nan sannu a hankali tana zama kasa mai jam’iyya daya tal tilo.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Tiransifomar wani bangare na Kinkinau ta lalace, na kuma ji jiya sun yi taro da yanke shawarar kowanne gida zai biya naira dubu biyar, a tara a sayo wata. Tirkashi! Tabdijan! Ashe ba an ce ba ruwan talakan da ake zalunta biyan kudin zama a duhuda gyara wa kamfanin wuta kayayyakinsa ba? Kamar fa eriyar MTN ko Airtel ta lalace ne a unguwarku, sai ku bi gida-gida kuna karbar kudin gyara wa kamfanin eriyarsa. Ga duka ga tsinka takalmi. Ba ka sha wuta ba, a tilasta maka biyan kudin zama a duhu, kayansu ya lalace ka gyara musu ai sai kasata Nijeriya ake yin wannan? Af har yau ban fa ji daga Pantami ministan sadarwa ba ko dai in hakura ne wato kai dai a yi sha’ani an cuci na kauye? Na sayi katin AIRTEL ya zama gaibu, na yi korafi shiru har yau?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply