Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 15.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 15.08.2019

66
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, goma sha biyar ga watan Zulhijja/Zulhaj, shekarat 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha shida ga Agustan 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ci gaba da kaddamar da ayyuka a jihar Katsina, har da asibitin mayakan sama a Daura.

2. Shek El-Zakzaky na kan hanyarsa ta dawowa gida Nijeriya daga Indiya sakamakon takaddamar da ta taso tsakaninsa da gwamnati a kan jinyar da ya je yi Indiya ranar litinin tare da matarsa.

3. Hukumar EFCC ta kaddamar da binciken shugabar ma’aikata ta kasa Winifred Oyo-Ita saboda zargin ta yi wata damfara ta naira biliyan uku.

4. Wadanda suka sace shugaban cocin babtis a Kaduna, sun yi ragi daga naira miliyan ashirin, sun sauko zuwa naira miliyan goma.

5. Sojoji a kalla uku aka kashe a lokacin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai farmaki wani sansani na Mammanti da ke jihar Barno.

6. Hukumar ‘yan bautar kasa NYSC a takaice ta ce duk jabun dan bautar kasa da ta kama daurin shekara biyu ne a gidan yari.

7. Gobe asabar idan Allah Ya kai mu a nan Kaduna Salisu Salinga zai gudanar da wani gangamin wayar da kai a kan sabon gidan talabijin nasa da ya bude ta kafar yutub/Youtube, da nake daya daga cikin wadanda za su gabatar da lakca a wajen.

Mu wayi gari lafiya.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply