Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 15.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 15.08.2019

58
0

Assalamu alaikum, barkanmu da asubahin alhamis, goma sha hudu ga watan Zulhijja/Zulhaj, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha biyar ga Agustan 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan kudirin sauya sunan NIGERIAN PRISON SERVICES, zuwa NIGERIAN CORRECTIONAL SERVICES ya zama doka. Wato daga hukumar kula da gidajen yari, a yanzun sunan ya zama hukumar kula da gyara hali.

2. Hukumar da aka kafa don binciken zargin da ake yi wa sojoji sun kashe ‘yan sanda uku da farar hula daya bayan sun kamo Hamisu da ake zargin rikakken kidinafa ne a jihar Taraba, ya kama sojoji biyar har da wani jagoransu kyaftin, da wasu ‘yan sanda biyu sai farar hula da dama da suke da nasaba da Hamisu da ko dai su ma an kamo su, ko sun tsere.

3. A jihar Ogun ana zargin wasu sojojin hudu sun bindige mutum uku sun mutu, sai dai sojojin sun ce kiransu aka yi su kawo dauki, kuma a saninsu ba su kashe kowa a wajen ba.

4. Wasu ‘yan fashi sun sace wata rabaran sista a jihar Binuwai.

5. Kungiyar kiristoci CAN ta ce ta soma magana da wadanda suka yi kidinafin mai wa’azi na cocin baptist a Kaduna Elisha Numan, inda suka ce sai an ba su naira miliyan ashirin kafin su sako shi.

6. Mai martaba sarkin Zazzau ya yi korafin talaka na dandana kudarsa a wannan zamani.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Mutane da dama idan mun hadu sai su ce suna jin dadin rubutun da nake yi kuma sukan so su yi tsokaci amma suna tsoro. Saboda duk abin da suke nema musamman mukamai na siyasa idan suka yi tsokaci a rubutuna sai a hana su, a dauko musu tsokacin da suka yi a rubutuna musamman idan ina yin cakulkuli a ce ga fa tsokacin da suka yi a dandalin Guibi na taya bera buruntu. Saboda haka sun lashe cokalinsu.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply