Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 16.09.209

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 16.09.209

93
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, goma sha shida ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha shida ga Satumba na 2019.

  1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa shugabannin kasashen yammacin Afirka shawarar su kokarta a ta kowacce fuska don magance matsalar tsaro da ke addabarsu.

2.Gwamnatin tarayya ta amince da wata naira biliyan dari da sittin da shida don gyara wasu manyan hanyoyi na tarayya da ke sassan kasar nan guda goma sha hudu.

  1. Shugaban kasar Afirka ta Kudu Ramaphosa ya aika kasashen Afirka don ba su hakurin cin zarafin da ‘yan kasarsa suka yi wa baki.
  2. Gwamnan jihar Kano Ganduje ya ce shi fa sai ya gudanar da tsarin nan na samar da ruga.
  3. Gwamnatin jihar Taraba ta ce za ta samar da wani sintiri na hadin gwiwa don kawo karshen rikicin Munci da Jukunawa.
  4. Ana ci gaba da musayar wadanda gwamnatin jihar Katsina ta tsare da wadanda ke hannun kidinafas. Kidinafas sun sako mutum talatin a baya-bayan nan wa gwamnati don ta sakar musu wadanda ta tsare musu.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya na gani a fesbuk wani yana korafin buhun shinkafa a yanzun ya kai naira dubu ashirin da biyu. Ni dai na san a karshen watan Agusta na sayota naira dubu goma sha shida da dari biyar. A karshen watan Yuli na sayota naira dubu goma sha biyar. A karshen watan Yuli na sayota a naira goma sha hudu da dari biyar. Masu cewa ta kai naira dubu ashirin da biyu a yanzun, sun ce ‘yar Hausa/ta gida ita ce naira dubu goma sha takwas a yanzun.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply