Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 18.11.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 18.11.2019

93
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, ashirin ga watan Rabiul/Rabiyul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha takwas ga Nuwamba, na 2019.

1. Manyan labarun su ne na zaben gwamna na jihar Bayelsa, da bayanai ke nuna APC ta kwace jihar daga hannun PDP, sai na jihar Kogi, da sai da safiyar nan za a kammala tattara sakamakon da sanar da shi, da can ma bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, ke nuna Yahya Bello na APC ke kan gaba.

2. Lakcarorin nan guda biyu na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da namu na kwalejin foliteknik da kidinafas suka yi kidinafin a Kaduna, sun samu sun kubuto daga hannunsu bayan kusan kwana shida a hannun nasu.

3. Sojoji sun yi nasarar murkushe wasu ‘yan kungiyar Boko Haram, a Barno, suka ceto mutane da dama da ke hannunsu.

4. A Kaita da ke jihar Katsina, wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum biyu, suka kuma ji wa wani dan sanda rauni.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply