Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 19.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 19.08.2019

79
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, goma sha takwas ga watan Zulhijja/Zulhajj, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha tara ga Agustan 2019.

1. A yau litinin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da taron sanin makama ga sabbin ministoci da zai nada.

2. Sabon kwamandan rundunar Lafiya Dole da ke fafatawa da kungiyar Boko Haram Manjo Janar Gabriel Olusegun ya ce a nasa tsarin sojoji sun daina zama suna jiran sai kungiyar Boko Haram ta kai musu hari, su mike suna kokarin kare kansu ko mayar da martani. A yanzun za su dinga bin ‘yan kungiyar ne a duk inda suke suna yakarsu har sai sun gama da su gabadaya.

3. A Katsina-Ala da ke jihar Binuwai wasu al’u’momi biyu sun yi fada har an kashe mutum a kalla tara.

4. Majalisar Dattawa ta ce ba ta ji dadin wulakancin da masu goyon bayan kungiyar Biafra suka yi wa Sanata Ekweremadu a Jamus ba.

5. Samson Siasia ya ce bai yarda da hukuncin da FIFA ta masa ba don bai aikata laifin da ake zargin ya aikata ba, kuma yana nan tare da lauyoyinsa yana shirin kalubalantar hukuncin da FIFA ta masa na hana shi wasa har ya koma ga ubangijinsa.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Wanda ya bude dandalin fesbuk da sunan DITV da Alheri Radiyo har yake wallafa labaru na kage, da har hukumomin tasoshin ke namansa tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, ya fito ya ba da hakuri cewa kuskure ne a yafe masa ba zai kara ba, ya ma rufe wannan dandali. Shi kuma mamallakin DITV da Alheri rediyon Dafta Hakeem Baba-Ahmed nan take ya ce ya yafe masa.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply