Home Sabon Labari Taskar Guibi> Labarai da Sharhi A Takaice

Taskar Guibi> Labarai da Sharhi A Takaice

71
2

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”p4x8y93yyv” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”e5xt7ah4mc” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”h0yn7l95kl” animation_delay=”0″]

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, ashirin da shida ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. da ya zo dai-dai da ashirin da shida ga Satumba na 2019.

1. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo ya ce a shirye yake ya cire rigarsa ta kariya don wanke sunansa daga zargi daban-daban da wasu suka dage suna masa. Ya kuma soma daukar matakai shari’a.

2. A yanzun haka shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, da ministan shari’a Malami, da ministan labaru Lai Mohammed, da gwamnan babban bankin Nijeriya da shugaban hukumar EFCC Magu, duk suna Landan suna kokarin nuna damfarar Nijeriya aka yi a hukuncin da kotun Landan ta yanke na P&ID na Nijeriya sai ta biya dala miliyan tara da rabi da ‘yan kai.

3. Femi Falana ya yi korafin duk da sun cika sharuddan sakin Sowore, har zuwa jiya da daddare ba a bi umarnin kotu an sako shi ba.

4. Wasu ‘yan bindiga a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna sun kashe mutum daya, suka yi kidinafin mutum a kalla goma sha hudu.

5. Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar talata mai zuwa a matsayin ranar hutun waiwayar ranar samun ‘yancin kan Nijeriya.

6. Shugabannin kwadago sun ce dauke Kiyamo da aka yi daga ma’aikatar Neja Delta zuwa ma’aikatar kwadago na iya saukaka tattaunawarsu a kan sabon albashi da gwamnatin tarayya.

7. Majalisar Dattawa ta yaba da rufe kan iyaka da aka yi, a Majalisar Wakilai har wasu sun yunkura kan sai an yi bincike a kan rufewar, mafi rinjaye suka yi fatali da kudirin.

Mu wayi gari lafiya.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

2 COMMENTS

Leave a Reply