Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 20.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 20.08.2019

71
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, goma sha tara ga watan Zulhijja/Zulhajj, shekara ta 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin ga Agustan 2019.

1. Gobe laraba idan Allah Ya kai mu shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rantsar da sabbin ministoci, bayan taron sanin makama da aka shirya musu jiya da yau.

2. Ofishin jakadancin Nijeriya da ke Jamus ya ce ya fara daukar matakan hukunta wadanda suka ci zarafin sanata Ekweremadu, har shi jakadan ya ce ba a sanar da ofushinsa Ekweremadu zai halarci taron na Inyamurai a Jamus ba, da tun farko an masa alfarmar motar ofishin jakadanci da ke da matakan tsaron da babu wanda ya isa ya keta masa rigar mutunci kamar yadda aka masa.

3. Fadar shugaban kasa ta nemi Babatunde Fowler shugaban hukumar tara kudaden shiga na cikin gida FIRS ya yi bayanin dalilan da suka sa, kudaden da hukumar ke tarawa a baya-bayan nan kullum sai baya, maimakon gaba.

4. Wata kotu ta dakatar da hukumar yaki da rashawa ta ICPC daga ci gaba da karbe kayan/kaddarori/dukiyar tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul Aziz Yari.

5. A Katsina wasu da ake jin barayin shanu ne sun kashe mutum uku suka saci shanu, amma an ce an bi su an kwato shanun, barayin sun gudu.

6. A Legas a wata kasuwa an dan bai wa hammata iska, aka lalata dukiya ta miliyoyi naira a lokacin da wani fada mai kama da na kabilanci ya kaure tsakanin Hausawa da Yarbawa.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Sai in ta jin labarin idan yaranmu da ke gama makaranta na neman aiki, sai sun ba da cin-hanci kudi tsugugu kafin a dauke su. Misali jiya na zauna wajen wani mai shagon shiga intanet, sai wani yaro ya zo zai cika takardar daukar aikin sibildifes. Sai mai wajen ya tambayi yaron nawa aka ce ya kawo cin-hanci na ji ya ambaci kusan naira dubu dari. Nan na ji ana ce masa an masa sauki, shi mai wajen intanet da ya cika nasa, an ce sai ya kai naira dubu dari biyar. Nan nake jin zargin cewa in za ka shiga kwastam sai ka ba da cin-hancin naira miliyan daya. Haka ma aikin dan sanda ko soja kwas na gajeren lokaci, na ma ji sun ce kwanakin baya da za a dauki aiki a wata kwaleji mallakar gwamnatin jihar Kaduna, ba karamin cin-hanci aka karba ba. Wasu wuraren ma an ce in ka samu aikin to albashin wata shida na farko ba naka ba ne. Na manya ne. Sai a wata na bakwai za ka soma ganin dilin-dilin.
a. Ina gaskiyar wannan zargi?
b. Baba Buhari ya sani kuwa?
c. Majalisar Dattawa ta sani kuwa?
d. Majalisar Wakilai ta sani kuwa?
e. EFCC da ICPC sun sani kuwa?
f. Ina sauran kungiyoyin matasa da lauyoyi suna sane kuwa?
Aff! Na ma ji ana zargin su kansu wadanda aka zaba ministoci sai da suka ba da cin-hanci ba kadan ba. Su kansu hukumomin irin su EFCC ana zargin kafin mutum ya samu aiki a wajen sai ya ba da cin-hanci.
KADA A MANTA DUK FA ZARGI NA CE ANA YI. Kada wani ya je ya ce Guibi ya ce ana karbar cin-hanci a ce in kawo shaida ba ruwana. Ji na yi ana fadi.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply