Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 21.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 21.08.2019

60
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, ashirin ga watan Zulhijja/Zulha, shekara ta 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da daya ga Agustan 2019.

1. Yau shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rantsar da sababbin ministoci da bai wa kowanne ma’aikatar da zai rike, bayan horo na sanin makamar aiki da suka sha shekaranjiya da jiya.

2. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya sanar ta bakin Frank Mba cewa sun sake samun nasarar damke Hamisu Bala Wadume a layin mai allo da ke unguwar Hotoro a jihar Kano. Har na ji Hamisun na cewa sojojin da suka kashe ‘yan sandan da suka damko shi da farko a Taraba, su suka kai shi can shalkwatarsu ta soja, suka balle ankwar da ‘yan sandan suka daura masa, suka ce ya tsere.

3. Hukumar yaki da rashawa da aka fi sani da ICPC ta damke wasu jami’an hukumar kula da kiyaye hadurra ta kasa FRSC su talatin da bakwai saboda zargin suna karbar na-goro a hannun masu ababen hawa da ke zirga+zirga.

4. Gwamnatin jihar Binuwai ta dakatar da wasu sarakuna uku saboda yadda fada ya ki ci ya ki cinyewa a yankin Katsina -Ala da ke jihar.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Na kuwa ji wasu na tonon kanawa cewa ba a cika kidinafin a Kano ba, amma an cika boye kidinafas ko wadanda aka yo kidinafin a can. Suka ce a Kano aka gano inda kidinafas suka boye Magajin Garin Daura, ga shi shekaranjiya litinin da daddare a Kanon aka gano Hamisu Bala da ake zargin rikakken gawurtaccen shararren gagararren wayayyen kidinafa ne.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply