Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 21.09.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 21.09.2019

75
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, ashirin da daya ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da daya ga Satumba na 2019.

  1. A dai-dai lokacin da wasu ke goyon baya wasu kuma ke tir da rufe kan iyakokin Arewa da gwamnati ta yi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce rufe bodojin kwalliya na biyan kudin sabulu. Sai dai na ji a shirin Ra’ayi Riga na BBC Hausa da suka yi jiya da daddare, ‘yan Arewa da suka koma shigo da motoci ta Legas saboda rufewar, sun yi korafin ba karamin kabilanci ake nuna musu a Legas din ba, kamar ‘yan Arewa ba ‘yan Nijeriya ba ne.
  2. Nijeriya na shirin zuwa Bankin Duniya ciwo bashin dala biliyan biyu da rabi da ‘yan kai.
  3. An raba dala biliyan dari bakwai da ashirin na watan Agusta tsakanin gwamnatin tarayya, da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, da ke nuna an kusan jin dilin-dilin.
  4. Shugaban Majalisar Wakilai Gbajabiamila ya nuna matukar bacin ransa da bayyana cewa zai je ya ga shugaban kasa Buhari da kansa ba sako ba, a kan ya kira shugabannin tsaro na kasar nan su yi taro a kan matsalar tsaro, shugaban ‘yan sanda, da na DSS da sauransu kowa ya je amma shugabannin sojoji, na tsaro gabadaya, da na sama da na kasa da na ruwa sai suka aike da wakilai, su suka ki zuwa. Saboda haka ya dage taron sai litinin.
  5. ‘Yan sanda a jihar Ribas sun yi nasarar kama mutumin da ya kware wajen kai mata otel ya kashe su. Ya ce tabbas shi ya kashe mata bakwai cikin takwas da aka ce an kashe. Da suka tambaye shi dalili sai ya ce haka kawai yake sha’awar ya kai mace hotel ya biya bukatarsa, in ya gama ya kashe ta.
  6. Babban bankin Nijeriya ya ba gwamnatin tarayya shawarar ta sayar da kaddarorinta da ke zaman banza ba sa kawo mata ko taro.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Kusan mako na hudu ke nan katin nan da na saya na wuta na naira dubu daya bai kare ba har yanzun. Saboda ba a kawo wutar, kuma ko an kawo ko dai ba karfi, ko ka ga wasu suna da wutar mu ba mu da ita. Kamar yadda na yi bayani kwanakin baya, makwabtana da ba su da irin mitata ta iya-kudinka-iya-shagalinka, ana cutarsu da suke biyan naira dubu biyar zuwa shida zuwa bakwai a karshen wata. Don a zahiri wutar da suke sha a wata ba ta kai ta naira dubu daya ba.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply