Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 23.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 23.08.2019

67
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, ashirin da biyu ga watan Zulhijja/Zulhaj, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhamnad S.A.W. Dai-dai da ashirin da uku ga Agustan 2019.

1. Jiya aka yi rabon kudin da aka saba na duk wata, inda aka raba naira biliyan dari bakwai da sittin da tara da rabi da ‘yan kai na watan Yuli tsakanin gwamnatin tarayya, da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, da ke nuna alamun babu mamaki a soma jin dilin-dilin ranar litinin. Da ma hantsi ya dubi bakin ludayi saboda hidimar Sallah da aka sha.

2. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin ruwa a Zariya, da wani katafaren ginin da babban bankin Nijeriya ya gina wa makarantar karatun digiri na biyu/tsakiya da na uku/koli da ke jami’ar Ahmadu Bello da ke Samarun Zariya.

3. Kowacce jiha za ta soma biyan gwamnatin tarayya bashin da ta ci a wajenta, naira biliyan saba’in da biyar ban da jiha daya tilo da ba ta ci ba.

4. Wasu mutanen garin Gubio da ke jihar Barno sun shaidawa BBC Hausa cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun kai hari garin shekaranjiya, har jami’an tsaro suka gudu, sai dai ba su taba kowa ba, amma sun tara su, sun yi musu wa’azi, suka kuma kona duk wani abu da ya shafi gwamnati a garin. Sai dai a jiya hukumar soja ta fitar da sanarwar cewa sojoji sun dakile wani hari da kungiyar Boko Haram ta kai Gubio da Magumeri.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya na ga wani bayani da ke nuna idan mutum yana yanka abarba sala biyu ko uku yana sa wa a ruwan zafi da safe yana shan ruwan, za ta masa maganin cututtuka har da na sankara wato kansa.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply