Home Labarai TASKAR GUIBI: Labarai da Sharhi A Takaice 23.10.2019

TASKAR GUIBI: Labarai da Sharhi A Takaice 23.10.2019

70
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, ashirin da hudu ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da uku ga Oktoban 2019.

 1. Gwamnatin tarayya ta yi sautun sabbin taragan/taragon jirgin kasa guda ashirin da ake sa ran isowarsu a watan gobe idan Allah Ya kai mu.
 2. Gwamnatin tarayya za ta sayo sabbin jiragen yaki na sama, da sauran makamai daga hannun kasar Rasha.
 3. Sojojin sama sun ci gaba da yin luguden wuta a Bukar Meram da ke jihar Borno, bayan sun hango ‘yan Kungiyar Boko Haram suna karakaina.
 4. Sojoji sun ce sun kama ‘yan kungiyar Boko Haram su goma sha hudu, har da kwamandojinsu biyu da ke cikin jerin wadanda suka fi nema ruwa a jallo.
 5. Sojojin sama sun ce sun soma bincike a kan zargin kashe wasa fararen hula biyu a kan wata budurwar sojansu a Sakkwato.
 6. Iyalan ‘yan sandan nan da suka kamo Hamisu da ake zargin rikakken kidinafa ne, sojoji suka kashe su bayan sun kamo shi a jihar Taraba, sun soma korafin sun ji maganar shiru.
 7. A Zariya an gano wasu cibiyoyin gyara hali guda biyu, aka ceto mutum goma sha daya, har mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna ta je wajen da kanta.
 8. Kotu ta ba da umarnin a karbe wasu kaddarori guda ashirin da uku na dan wani lokaci ko wucin gadi na Abdulrasheed Maina.
 9. Hukumar ICPC mai yaki da rashawa na neman Okoi-Obla ruwa a jallo saboda zargin ya tabka badakala daban-daban.
 10. Kotu ta sa biyu ga watan Disamba don yanke hukunci a kan zargin da EFCC ke yi wa tsohon gwamna Orji Kalu ta ya wawuri wata naira biliyan bakwai da rabi da ‘yan kai ta jihar Abia/Abiya, kudin da ya ce a lokacin da yake gwamna, jihar ba ta da arzikinsu.
 11. Kungiyar kwadago NLC ta ce dole fa sai an biya ma’aikata ariyas na wata biyar na karin sabon albashi mafi karanci da aka cimmawa.
 12. ‘Yan gudun hijira da suka koma gida Damasak da ke jihar Barno su fiye da dubu goma na bukatar agajin abinci.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya ko za ni Zariya na hango cincirindon ‘yan gudun hijira, da ‘yan bindiga da kidinafas suka tarwatsa kauyukansu a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, a filin makarantar firamare ta garin Birnin Yero. Abin gwanin ban tausayi ga sanyin safiya, ga goyo, ga tsofaffi da yara kanana, da mata. Wai ina abin yi ne? Don na so in ji dan majalisar wakilai mai wakiltar yankin na shaida wa BBC Hausa jiya da safe cewa shi kansa tsoron zuwa wajen yake yi kada kidinafas su yi ram da shi.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply