Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 26.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 26.08.2019

50
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, ashirin da biyar ga watan Zulhijja/Zulhaj, bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da shida ga Agustan 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar Japan/Jafan jiya don halartar wani taro na raya Afirka.

2. Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar da ke cewa matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati na nan, haka ma matsayin sakataren gwamnatin tarayya na nan, babu batun sai wani minista ko wani jami’in gwamnati ya kama kafar wani kafin ya iya ganin shugaban kasa ko makamancin hakan kamar yadda ake ta yadawa cewa shugaban kasa Buhari ya fadi.

3. Jam’iyyar APC ta kalubalanci Hamisu Wadume ya fito fili ya fallasa wadanda ya ce sun ba shi naira miliyan goma sha uku da sauransu a jam’iyyar ta APC don yakin neman zaben shugaban kasa Buhari na 2019.

4. Sojojin sun kama wasu motoci shida na yaki na soja za a wuce da su ta kasar nan ta kan iyakar Nijeriya da Camaru/Kamaru, sun mika wa hukumar kwastam su.

5. An bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta kona gidaje saba’in da uku, da shaguna ashirin da takwas a Kunduga.

6. Hafsoshin soja sun shiga garin Gubio da Magumeri suna lallashin jama’ar garuruwan, su koma su yi zamansu ba abin da zai kuma aukuwa gare su.

7. Sanata Ekweremadu ya ce ya yafewa wadanda suka wulakanta shi a Jamus.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Can na ga labari na ta karakaina a soshiyal midiya cewa gwamnan jihar Rivers/Ribas Wike ya rusa wani masallaci da ke jihar. Ina gaskiyar labarin?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply