Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 28.07.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 28.07.2019

92
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, ashirin da biyar ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da takwas ga Yulin 2019.

Da yaka karshen mako ne labarun sukan yi karanci a wasu lokuta irin wannan, ga wani labari da na kalato kuma nake ganin yana da muhimmancin gaske a wannan lokaci.

ROMANIA/ROMANIYA

An kori babban shugaban ‘yan sanda na kasar Romaniya daga aiki bayan kisan/kisar da aka yi wa wata ‘yar budurwa mai shekara goma sha biyar, da ta kwashe sa’a uku tana kiran ‘yan sanda a waya, su kai mata agajin gaugawa/gaggawa , ba su agajeta ba har kidinafas suka kasheta.
Nicholas Moga ya ce an kori shugaban ‘yan sandan kasar daga aiki ne, saboda sakacin da ‘yan sanda suka nuna har aka kashe yarinyar.
Rahotanni na cewa a ranar larabar da ta gabata, aka yi kidinafin budurwa, inda ta kokarta ta kira wayar agajin gaugawa ta ‘yan sanda don su kai mata dauki har sau uku, da musu bayanin inda take.
Iyayen yarinyar suka ce ‘yan sandan ba su dauki kiran nata da muhimmanci ba, , har aka kasheta. Sai dai ‘yan sandan sun kare kansu da cewa sun ta kokarin gano inda yarinyar take amma abin ya ci tura.
A karshe ake kyautata zaton ta mutu ne a hannun kidinafas, ya kuma sa aka kori shugaban ‘yan sanda na kasar gabadaya.

Mai karatu ya lamarin yake a kasarku?

Mu yini lafiya.

Af! Wutar lantarki a Nijeriya sai ci gaba da tabarbarewa take yi. Da rana a ba ku wutar sa’a biyu, da dadddare
wutar sa’a uku. A sa’a ashirin da hudu a ba ku wutar sa’a biyar, a hana ku ta sa’a goma sha tara. Toh! Ka ga laifin dan fulani da za shi aikin Hajji ya sayo tocila zai sa cikin kayansa wai saboda idan ya je Saudiya aka dauke wuta ya haska?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply