Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 28.09.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 28.09.2019

69
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, ashirin da takwas ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da takwas ga Satumba, na 2019.

  1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baro Niyok zuwa gida Nijeriya bayan halartar taron Majalisar Dinkin Duniya.
  2. Kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN ta ce tana tare da mataimakin shugaban kasa Osinbanjo, a wannan lokaci da suke zargin an tasa shi a gaba da zargin ya wawuri wata naira biliyan casa’in da ake zargin ya karba daga hukumar tara kudaden shiga a lokacin yakin neman zabe.
  3. Kotu ta amince a karbe duk wata kaddara da ke da nasaba da tsohuwar shugabar ma’aikata Winifred Oyo-Ita.
  4. Sojoji sun dakile wani yunkurin hari da kungiyar Boko Haram ta kai jiya Bale Shware kilomita uku daga Maiduguri, da ke kusa da barikin sojoji na Giwa.
  5. ‘Yan sanda na ci gaba da kama kidinafas da suka kashe mutane da dama a jihar Binuwai suka bisne su a manyan ramuka, suka shuka rogo da sauransu a wajen.
  6. Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya kai wa gwamna Nasir El-Rufai ziyara fadar gwamnati ta Sa Kashim Ibrahim da ke nan Kaduna.
  7. A Kadunar an kai mutane dari uku da ‘yan sanda ke zargin an tsare su ana cin zarafinsu da sunan gyara hali sansanin alhazai da ke Mando, bayan an kai su filin wasa na Ranchers Bees, don ci gaba da bincike.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Yau ashirin da takwas ina labarin dilin-dilin ne? Don na ji wasu ma’aikata suna ta wayyo Allah ga hidimar komawar yara makaranta an sha ga dilin-dilin shiru.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply