Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 29.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 29.08.2019

66
0

Assalamu alaikum asubahin alhamis ce ashirin da takwas ga watan Zulhijja/Zulhaj, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da tara ga Agustan 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ci gaba da karbar bakuncin shugabannin kasashen duniya a masaukinsa da ke Yokohama a Japan/Jafan, inda a baya-bayan nan ya karbi bakuncin shugaban kasar Binin/Benin Talcon, suka yi kus-kus-kus a kan rufe kan iyakar Nijeriya da Binin da kasar nan ta yi saboda korafin ana hauro da shinkafa ta can, ya kuma yi kus-kus-kus da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a kan cin zarafin da ake yi wa ‘yan Nijeriya a can.

2. Ana nan ana ta siyasar Visa/Bisa tsakanin Amurka da Nijeriya.

3. ‘Yan sanda sun yi albishir cewa an sako dalibai uku na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da aka yi kidinafin. Da ma labari ya bulla cewa masu garin da wasu ke zargin sun gagari gwamnatin Baba Buhari, sun ci gaba da tare hanyar Kaduna zuwa Abuja, har a jiya suka yi kidinafin wasu mutum shida, har da dalibai uku na A.B.U. Iyaye da jami’ar suka fitar da sanarwar suna nan a jiyan suna kokarin ganin an sako su. Can zuwa yamma kuwa sai ga sanarwar daga ‘yan sanda cewa an sako su. Sai dai na ji wasu na tambaya. ‘Yan sanda ne suka karbo su, ko suka kubutar/ceto su, ko jami’ar ce ta biya kudin fansa, ko iyayen yaran?

Mu wayi gari lafiya.

Af! Can na ga wani labari na karakaina a fesbuk cewa albashin da gwamnan jihar Kaduna zai kara wa ma’aikatan jihar Kaduna na naira dubu talatin mafi karanci, daga watan gobe, su malaman makaranta nasu ya ma fi naira dubu talatin mafi karanci.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply