Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 29.09.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 29.09.2019

84
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, ashirin da tara ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da tara ga Satumba, na shekarar 2019.

  1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iso gida Nijeriya daga babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ya halarta a Niyok.
  2. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai ji dadin rahoton da ya samu daga Kaduna na an tsare yara da manya su wajen dari uku da ake zargin cin zarafinsu da sunan gyara hali ba. Ya yaba wa jami’an tsaro da suka ceto yaran. Sai dai wasu mata daga cikin iyayen yaran sun bayyana cewa suna goyon bayan tarbiyyar da ake koyarwa a makarantar shi ya sa ma suka kai ‘ya’yansu.
  3. Kwamitin Majalisar Wakilai ya soma rangadin sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Barno.
  4. Jami’an imagireshan sun ce sun kama wasu ‘yan kasar Nijar su biyu da makamai a wuraren kan iyakar Katsina.
  5. Ana nan ana ci gaba da shirye-shiryen bikin cika shekara hamsin da tara da samun ‘yancin kan Nijeriya.
  6. An bisne gawar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Nepa suna kokari fiye da kwanakin baya, tun dai da ministan lantarki ya zo Kaduna wutar ta dan inganta. Don katin naira dubu daya da na ce yana kai mun wata daya, wani lokaci har wata daya da rabi, to a yanzun kwana shida zuwa bakwai ya kare. Da ke nuna in wutar ta dore a haka duk wata zan sayi katin naira dubu hudu zuwa biyar. Ka ga idan ba ka da irin mitata ta iya-kudinka-iya-shagalinka, Nepa suka kawo maka takardar biyan kudin wuta, ka ga sun sa naira dubu hudu ko biyar, to ka biya ta hakan ka sha, ba cuta ba cutarwa. Amma fa a unguwarmu. In kuwa suka kawo maka naira dubu bakwai ko takwas ka ce kana da ja.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply