Home Sabon Labari TASKAR GUIBI: Labarai da Sharhi A Takaice 29.10.2019

TASKAR GUIBI: Labarai da Sharhi A Takaice 29.10.2019

78
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, talatin ga watan Safar, TUNDA HAR ZUWA YANZU KARFE BIYAR SAURA BAN SAMU LABARIN AN GA JINJIRIN WATAN RABIUL /RABIYUL AWWAL BA, shekarar 1441, bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. In an gani na sauya/canza kwanan watan, dai-dai da ashirin da tara ga Oktoban shekarar 2019.

  1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi Saudiya domin wakiltar Afirka wajen taron zuba jari da bunkasa tattalin arziki. Daga nan zai wuce London/Landan. Ana dai ci gaba da tabka muhuwara a kan ziyartar kasashen duniya da shugaban kasa ke ta yi, tsakanin magoya bayansa da ‘yan adawa.
  2. Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta je Majalisar Dattawa da ta wakilai don sanar da shugabannunsu cewa ba fa za su amince a tilasta musu shiga tsarin nan na IPPIS na biyan ma’aikata albashi da sauran hakkokinsu kai tsaye daga Abuja ba. Ahmed Lawan shugaban majalisar ta dattawa ya ba su tabbacin duba lamarin.
  3. Emefiele ya ce masu tunanin bude bodojin kasa na kasar nan a yanzun su ma daina don ba za a bude ba.
  4. Yarbawa sun ce suna nan a bayan Osinbanjo ba gudu ba ja da baya.
  5. Gwamnonin jihohi sun ce za su iya biyan mafi karanci albashi ne, ga ma’aikatansu, kowacce jiha dai-dai karfin samunta na kudaden shiga.
  6. Wani dan sanda ya kashe matarsa ya kashe kansa.
  7. Mutum dari da goma sha daya Allah Ya yi wa rasuwa a jihar Katsina sakamakon cutar yalofiba.
  8. Shugaban Majalisar Dattawa ya ce yau kowa zai karkare kare kasafinsa, majalisar ta gabatar da rahoto ranar ashirin da takwas ga watan gobe.
  9. Wutar lantarki na ci gaba da tabarbarewa. Ko an kawo ta ba ta da kumari.
  10. Ruwa a rafin gadar Hayin Malam Bello da aka yi shekaranjiya da yamma zuwa dare ya yi sanadiyyar rasuwar wata budurwa da ke raba katin aurenta.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Sojojin sama sun kaddamar da atisayen da suka radawa suna NA ZO a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, da kuma Kaduna zuwa Abuja. Don jin tarihin irin wadannan sunaye da sojoji ke sa wa ko rada wa atisayensu, da tasirinsu, a nemi kundin makaloli na bincike mai suna KADAURA na sashen nazarin harsuna na jami’ar jihar Kaduna, da ya fito makon jiya, don karanta makalar da na rubuta a kai. Sannan a wancan kundin nasu na musamman kafin wannan, na yi rubutu a kan bambace-bambance fassara a gidajen rediyo da talabijin na wannan karni.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply