Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 30.07.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 30.07.2019

83
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, ashirin da bakwai ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da talatin ga Yulin 2019.

 

1. Jiya da yamma sojoji sun yi nasarar dakile wani hari da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yunkura kaiwa wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke Bama. An ce ‘yan kungiyar sun aike da takardar gargadin suna nan zuwa su kwashi mata da yara. Babu mamaki labarin wannan wasika ya kai ga sojojin, ya sa suka kasance cikin shiri.

2. Sai dai kafin jiyan, ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun kashe fiye da mutum sittin da biyar a jihar ta Barno, har ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin sai an kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika.

3. Haka nan a makon da ya gabata ‘yan bindiga a Zangon Kankara da Makera, da ke jihar Katsina sun kashe mutum ashirin da biyu, suka kwashi matan aure da ‘yan mata goma sha takwas.

4. A Birnin Kabbi ma ‘yan bindiga da wuraren karfe biyun dare sun kashe mutum kusan sittin da biyar.

5. Ranar litini mai zuwa, biyar ga watan gobe na Agusta kotu za ta yanke hukunci a kan batun kyale Shek Alzakzaki ya je jinya kasashen waje.

 

 

Is’haq Idris Guibi
Kaduna, Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply