Home Labarai Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 30.09.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 30.09.2019

95
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin daya ga watan Safar, shekara ta 1441 bayan hijirar cikamakin annnabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da talatin ga Satumba, na 2019.

  1. A Kaduna an sha ruwan sama. Tun jiya da daddare wuraren karfe tara aka soma ruwan har zuwa safiyar nan kuma ana yi.
  2. Sojoji na ankarar da jama’a cewa idan sun ji rugugi na wuta da amon bindiga kada su tsorata, domin hakan na daga cikin bikin cika shekara hamsin da tara da samun ‘yancin kan Nijeriya da za a yi gobe talata daya ga watan Oktoba idan Allah Ya kai mu.
  3. Majalisar wakilai ta ce za ta bibiyi kudaden da ake hankada wa hukumomin tsaron kasar nan don bincikar hanyoyin da suke bi wajen kashe su.
  4. Jami’an hukumar kula da kiyaye hadurra sun kama wani fasinja da bindiga kirar AK47 a jihar Taraba.
  5. Kidinafas sun sako mahaifiyar Samson Siasia bayan ta kwashe kwanaki a hannunsu, da biyansu kudin fansa ko ajiyarta. Sai dai an ce wanda ya kai kudin sun rike shi suka sakota, shi ma sai da aka biya nasa sannan aka sako shi amma fa a jihar Bayelsa.

Jama’a labarun ke nan saboda hutu ne na karshen mako labarun kan dan yi karanci.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Me ma zan ce ne ma?
Ai kuwa an ce mun an so a ji famfo a unguwar Kinkinau Kaduna na hucin kawo ruwa jiya wuraren la’asar, bayan kusan shekara daya rabonmu da mu ga ruwan famfo. Saukin abin su ba sa zuwa su ce sai an biya kudin ruwan da ba a sha ba ko ba a kawo ba irin yadda su wa’e suke yi na biyan kudin zama a duhu.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply