Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 31.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 31.08.2019

79
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, talatin ga watan Zulhijja/Zulhaj, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakun annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da talatin da daya ga Agustan 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin Jukun da Munci/Tibi da su tabbatar da sun kawo karshen rikicinsu da ya ki ci ya ki cinyewa, tare da nuna rashin jin dadinsa da kisan da aka yi wa wani mai wa’azin coci David Tanko a Taraba, kisan da ke da nasaba da rikicin.

2. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu ya bai wa ‘yan sanda umarnin su farauto masa wadanda suka kashe David, tare da gaisuwar mutuwarsa. Har ila yau shugaban na ‘yan sanda ya ba da umarnin jiragen ‘yan sanda masu saukar ungulu su dinga shawagi a wasu manyan tituna ciki har da hanyar Kaduna zuwa Abuja don maganin makasa da kidinafas.

3. Kidinafas sun sace dan majalisar dokoki ta jihar Kaduna mai wakiltar Zariya Suleman Ibrahim Dabo a hanyar Kaduna zuwa Zariya. Daga baya bayanai na nuna an sako shi. Haka nan a Abuja an yi kidinafin shugaban jam’iyyar A.C. na kasa bakidaya Kenneth. Su ma mutanen Rigasa da ke Kaduna kidinafas ne ke ta sace musu mutane musamman matan aure har da masu juna biyu.

4. A Kadunan dai a kauyen Kiri da ke yankin karamar hukumar Kaura, jaridar Daily Trust ta ba da rahoton an kashe mutum biyar aka kona gidaje.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Mutanen Zariya sun shiga mawuyacin hali a kan kin karbar kudin da suka yage ko suke da huji ko liki.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply