Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labaran Duniya A Takaice 03.12.2019

Taskar Guibi: Labaran Duniya A Takaice 03.12.2019

87
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, shida ga watan Rabiul/Rabiyul Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da uku ga watan Disamba, na 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aza tubalin gina jami’ar karatun al’amuran sufuri, a yankin karamar hukumar Sandamu da ke Daura a jihar Katsina. Gina jami’ar na cikin yarjejeniya guda uku da aka yi da kamfanin kasar Sin/Caina/China da ya yi kwangilar aikin dogo/jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja. Wato bayan aikin jirgin, zai kai ‘yan Nijeriya kasar Sin su yi digirori bangaren yin jiragen, da gyara shi da sauransu. Sai bangare na uku zai gina jami’ar sufuri da idan ‘yan Nijeriyan sun dawo za su yi aiki da abin da suka koyo a jami’ar. Na ji Amaechi na nanata shi ya zabi a gina jami’ar a Daura ba wani ba, ko kuma wani ya yi kamun kafa ba.

2. Gwamnatin tarayya ta ba da tabbacin ba za a yi wahalar mai a karshen shekarar nan kamar yadda aka saba a lokacin kirsimeti da sabuwar shekara ba.

3. Jiya auren shugaban kasa Muhammadu Buhari da Hajiya Aisha Buhari ya cika shekara talatin da daurawa. Wato shekararsu talatin suna tare.

4. Kotu ta yi watsi da kalubalantar ikon da shugaban ‘yan sanda ke da shi na daukar ‘yan sanda aiki. Hukumar kula da al’amuran ‘yan sanda PSC a takaice ce, ta kalubalanci ikon, kotu ta yi watsi da kalubalantar.

5. Kotu ta karbe muhallalin tsohon shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da ke Ilori, gidan da ya ci naira biliyan daya wajen gina shi, karbewa ta wucin gadi ko na dan wani lokaci. EFCC na zargin an gina gidan ne da kudaden gwamnati da aka wawura ko aka tara su ta hanyar kamiyamiya.

6. Jami’an tsaro na DSS sun ceto wasu yara ‘yan Zuru su biyu, daga hannun masu satar yaran Arewa suna kai su kasashen Inyamurai suna sauya/canza musu suna da addini.

7. Kotun Afirka ta Kudu ta yake wa wani dan sanda da ya kashe wani dan Nijeriya a watan Janairu na shekarar 2018 hukuncin daurin shekara talatin

8. Hukumar EFCC ta karbe fasfon Onyeama mamallakin kamfanin Air Peace da Amurka ke zargin dan damfara ne.

9. Hukumar imigireshan ta ce wa’adin da ta ba bakin haure na su tarkata inasu-inasu su bar kasar nan, nan da goma sha biyu ga watan gobe yana nan.

10. Gwamna Ganduje ya sake aike wa majalisar dokoki ta jihar Kano kudirin dokar yin sabbin masarautu guda hudu daga masarautar Kano. Kotu ta soke dokar farko da ta kirkiro masarautun saboda rashin bin ka’ida, shi ne gwamnan ke so ya bi ka’idar a yanzun.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply