Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, ashirin da biyu ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da biyar ga Yulin 2019.
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Muhammad Tanko a matsayin sabon babban mai shari’a na kasar nan.
- Majalisar Dattawa a jiya ta tantance goma daga cikin sunayen wadanda shugaban kasa ya aike mata don amince masa ya nada su ministoci. Yau majalisar za ta ci gaba da tantance sauran.
- Majalisar Dokoki ta Kasa za ta yi bincike a kan zargin wasu sojoji biyar da ke yakin harbin kunama karo na uku sun tsere da wasu biliyoyin naira.
- Hukumar EFCC ta rufe/like/toshe/hana Okorocha zuwa kusa da wasu kadarorinsa, da ke a Owerri, a jihar Imo.
- ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da manona goma sha takwas a jihar Neja.
- Dakaru sun kashe ‘yan bindiga saba’in da takwas a jihar Zamfara, da kwato wasu makamai.
- A yanzun Boris Johnson ya zama firaministan Birtaniya, har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike masa da sakon tayin murna.
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.
