Home Labarai Taskar Guibi: Labarun Duniya Da Sharhi A Takaice 26.07.2019

Taskar Guibi: Labarun Duniya Da Sharhi A Takaice 26.07.2019

116
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, ashirin da uku ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da shida ga Yulin 2019.

1. A jumar’ar nan shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci bikin cika shekara dari da saba’in da biyu da samun ‘yancin kan kasar Liberia/Laberiya, inda har za a girmama shi da lambar yabo mafi girma ta kasar.

2. Zuwa jiya Majalisar Dattawa ta tantance ashirin da hudu, saura goma sha tara, na wadanda shugaban kasa ya ba da sunayensu, don neman amincewarta ya nada su minista. Sai dai na ji wata al’umar da ke jihar Kaduna na korafin ba a nuna ana yi da su ba a sunayen wadanda aka tura don ba su mukamin minista.

3. Mace daya da maza biyar na kungiyar agaji ta ‘Action Without Hunger’da kungiyar Boko Haram ta yi awon gaba da su bayan ta kashe direbansu a jihar Barno, sun bayyana a wani faifan bidiyo suna rokon gwamnatin tarayya da kungiyoyi su ceto ransu daga hannun kungiyar ta Boko Haram. Sai dai bayan bayyanar bidiyon gwamnatin tarayya ta sanar cewa tuni ta fara tattaunawa da kungiyar don ceto ransu.

4. An raba naira biliyan dari bakwai da sittin da biyu, da naira miliyan dari biyar da casa’in da bakwai tsakanin gwamnatin tarayya, da jihohi da kananan hukumomi na watan Yuni, da ke nuna ma’aikata sun kusan soma jin dilin-dilin.

5. Kungiyar dalibai ta kasa ta rufe shalkwatar kamfanin sadarwa na MTN da ke Kaduna, saboda nuna fushinsu a kan kashe ‘yan Nijeriya su dari da goma sha takwas a Afirka ta kudu mamallaka kamfanin na MTN. Ba sabon labari ba ne yadda ‘yan Afirka ta kudu ke ci gaba da tsangwamar ‘yan Nijeriya da ke zaune a can a ‘yan shekarun nan.

6. Ana ci gaba da kidinafin da kashe mutane a jihar Kaduna. Na baya-bayan nan ita ce wata jami’a ta kotun shari’a da aka yi kidinafin a yankin Chikun bayan an kashe danta.

7. Wani maciji ya tarwatsa zaman majalisar dokoki ta jihar Ondo, a lokacin da suke kan zama ya fado musu daga sama.

8. A kasashen Turai ana tsananin zafin da aka shekara dari biyu rabon da a ji irinsa.

9. Korea/Koriya ta Arewa ta cilla wani makami mai linzami mai gajeren zango Teku.

 

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply