Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarun Duniya da Sharhi A Takaice 27.07.2019

Taskar Guibi: Labarun Duniya da Sharhi A Takaice 27.07.2019

91
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, ashirin da hudu ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da bakwai ga Yulin 2019.

1. Kasar Laberiya ta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari lambar girmamawa mafi girma ta kasar ta KGR a lokacin bikin waiwayowar ranar samun ‘yancin kanta da ta gudanar jiya a Monrovia/Manrobiya.

2. Zuwa jiya Majalisar Dattawa ta tantance mutum talatin da daya, daga cikin sunayen mutum fiye da arba’in da shugaban kasa ya tura mata don neman amincerta ya nada su ministoci. A wadanda aka tantance jiya akwai Malami da Keyamo.

3. An ceto turawan nan hudu ‘yan kasar Turkiyya da aka sace a jihar Kwara ba tare da an biya ko taro ba. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kayode ya ce da farko kidinafas da suka sace su, sun bukaci naira miliyan dari hudu, suka yi sauki zuwa naira miliyan dari daya. Sun sako turawan ne bayan an kama biyu daga cikin wadanda ake zargi da sace turawan.

4. ‘Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari wani sansanin ‘yan gudun hijira, da ke jihar Barno, suka kashe mutum biyu, suka ji wa da dama rauni.

5. Hukumar shirya jarabawa ta WAEC ta fitar da sakamakon jarabawarta ta 2019, da bayanin kashi sittin da biyar cikin dari na wadanda suka rubuta jarabawar sun ci har da darasin Ingilishi da na lissafi.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply