Home Sabon Labari Taskar Guibi: Sharhi da Labarai A Takaice

Taskar Guibi: Sharhi da Labarai A Takaice

72
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, shida ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da biyar ga watan Oktoba, na 2019.

  1. An ba da belin Sowore karo na biyu inda a wannan karon za a biya naira miliyan dari da kuma sauran wasu sharudda da kotun ta gindaya.
  2. Jama’a na ta tururuwa zuwa fadar basarake Soun na Ogomosho/Ogbomosho don ta’aziyyar mutuwar wani kunkuru da ya mutu bayan ya kwashe shakera dari uku da arba’in da hudu yana raye a duniya.

Jama’a sai a yi hakuri yau labarun biyu ne kacal saboda sun mana rowar wutar jiya zuwa yau da asubah. Har jinkirta rubutuna na asubahin nan na yi ko za su kawo da karfe hudu in karo wasu, har zuwa yanzun karfe biyar saura minti hudu ba su kawo wutar ba.

Mu wayi gari lafiya don da ma an ce da kyar na kai ya fi da kyar aka kama ni.

Af!
Ministan kwadago Chris Ngige ya ce in fa har sai an biya sabon albashi to da alamu sai an rage yawan ma’aikata gwamnatin tarayya tukuna don idan an yi karin kudin zai yi wa gwamnati yawa ba za ta iya biya ba. Sai dai na ji wasu na cewa za ta iya biya tunda shugaban hukumar kwastam Hameed Ali ya ce saboda rufe bodoji a kullum sai hukumarsa ta tara naira biliyan biyar. Ni ma na gan shi jiya a talabijin ya ce a watan Satumba kawai ya tara naira biliyan dari da goma sha biyar. Sannan a ce ba za a iya biyan sabon albashi ba? Ba fa a maganar kudin da ake samu na mai, da kudin da hukumar tara kudaden shiga ta cikin gida ke tarawa, da sauran hanyoyi na haraji. Kodayake wasu na zargin ‘yan Majalisar Dattawa kawai ke more dukiyar kasar nan daga irin kudaden da suke hankada wa kansu da kansu.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply