Home Sabon Labari Taskar Guibi: Takaitattun Labarai a Nijeriya 22.11.2019

Taskar Guibi: Takaitattun Labarai a Nijeriya 22.11.2019

91
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, ashirin da hudu ga watan Rabiul/Rabiyul Awwal, shekara ta 1441 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da biyu, ga Nuwamba, na shekarar 2019.

1. Babban labarin da yake ta karakaina a soshiyal midiya daga jiya zuwa yanzun, na kuma san shi zai kasance kanun yawancin jaridun kasar nan da za su fito da safiyar nan, shi ne labarin babbar kotun Kano ta ce dokar da ‘yan majalisar dokoki ta jihar suka yi, da ta ba gwamna Ganduje ikon kirkiro sabbin masarautu, ko sarakuna masu daraja ta daya, ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan. Kotu ta ce ‘yan majalisar ba su bi ka’ida ba, wajen yin dokar. Saboda haka dokar ba ta yi ba, haka nadin sarakunan bai yi ba. Da ke nufin an rushe nadin sarakunan guda hudu. Sai dai gwamnatin jihar ta ce za ta ci gaba da tafiyar da lamura da sarakunan da kotu ta rushe, har sai ta yi nazari a kan hukuncin. Gwamnatin jihar Kano na da kwana casa’in don daukaka kara kotu ta gaba, idan hukuncin bai mata ba. Wasu na murna da hukuncin, wasu ba sa murna da shi. Masarautun da gwamnan jihar Kano Ganduje ya mayar da su masu daraja ta daya daga ainihin masarautar Kano, su ne Rano, da Gaya, da Bichi, da kuma … A tuna mun ta hudun na manta?

2. Majalisar Dattawa ta amince a kara kudin haraji na tamanin kaya wato VAT daga kashi biyar, zuwa kashi bakwai da rabi daga sabuwar shekarar 2020.

3. Kidinafas na ci gaba da bin mutane gida-gida a cikin garin Kaduna, suna sace su. Na baya-bayan nan shi ne wadanda suka bi har gida suka kwasa a Hayin Dan Mani. Sun fi jidar mutane a Nariya, da Rigasa, da Mahuta, da Hayin Dan Mani. Ciniki yakan kaya daga miliyan goma zuwa ashirin, su ba ruwansu da kai talaka ne, ko mace mai ciki ko goyo da shayarwa. Duk tarkatawa suke yi.

4. ‘Yan sanda a jihar Kaduna sun ce sun kama wasu mutum bakwai da suke zargin barayin shanu ne, da kwato shanu guda dari biyu da saba’in da uku.

 

Af! A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau da za ta fito anjima da safe, don karanta rubuce-rubucen da na yi a soshiyal midiya, daga juma’ar da ta gabata, zuwa jiya alhamis. Godiya ga editanta Abdulrazak Yahuza Jere, da mai kamfanin sadarwa na Dutsen Kura Communication DCL Hausa, Zahradeen Umar, da mai dandalin ArewaDaily Post Ibrahim Ammani, da sauran dinbin jama’a, da na sani da wadanda ban sani ba, da ke buga, ko yada rubuce-rubucen nawa, zuwa dandali daban-daban. Sai gidajen rediyon da ke shirin ware wani sashe na musamman don karanta rubuce-rubucen nawa, da ma’aikatan rediyon da in suna aikin safe, sukan leka fassarata don sanin yadda za su fassara labarun da na fassara, don yawanci labarun da na bayar da asubah, su suke kicibis da su idan sun je aiki da safe cikin harshen Ingilishi.

is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply