Home Sabon Labari Taskar Guibi: Takaitattun Labarai da Sharhi 02.01.2020

Taskar Guibi: Takaitattun Labarai da Sharhi 02.01.2020

91
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, shida ga watan Jimada Auwal/Ula, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da biyu ga watan Janairu, shekarar 2020.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin ci gaba a wannan sabuwar shekarar, a bangarori daban-daban da suka hada da tattalin arziki, da tsaro, da siyasa, da zamantakewa da kuma yaki da rashawa. Ya kuma ba da tabbacin ba zai sa a yi gyaran kundin tsarin mulki domin ya yi ta-zarce daga shekarar 2023 ba.

2. Jarirai da aka soma haihuwa a sabuwar shekarar nan ta 2020 na ci gaba da shanawa daga matan gwamnoni, saboda kyaututtuka daban-daban da suka ba su.

3. Hmm! Ana fa sanyi don a yanzun haka da nake wannan rubutu karfe biyar saura kwata na asubah ina jin sanyin da iska suna ketawa. Zuwa anjima idan mun fita sallar asubah na san zan ga kusan kowa da hular sanyi da nadi, da riguna wasu biyar har zuwa sama. Ire-irenmu ne ba ruwanmu da sanyi in kuma akwai wanda ya taba ganina na fita da hular sanyi ko riga biyu sallar asubah ya fadi. Ga wani can na tambayar sirrin ko fahamin ko lakanin. To ni dai janar ne mai anini uku. Ko a kwallon dattawa da muka buga jiya a filin wasa na Ahmadu Bello da ke cikin garin Kaduna, sun dauka za a dauke ni ranga-ranga sai suka ga ba haka ba.

4. Sauran ma’aikatan gwamnatin tarayya da har zuwa yau biyu ga wata ba su ga sabon albashi ba ballantana ariyas na ci gaba da dako ko Allah Ya sa su dace. A yanzun dai saura wata uku su cika shekara daya da zaman jira kamar yadda aka musu alkawari za a biya daga watan Afrilu na shekarar 2019 da ta gabata. Ma’aikatan jami’o’i na tarayya da kwalejojin foliteknik na tarayya na cikin ma’aikatan da suke zaman jira.

Af! Abin mamaki jiya ina shawagi a fesbuk sai na ga wasu da ban san su ba, ko dai sun zabe ni gwarzonsu na shekarar 2019 ko kuma ina cikin jerin gwarazansu. Kadan daga cikin wadannan mutane da suka zabe ni su ne:
a. Abubakar M.Lawal Malumfashi
b. Sani Musa Richifa.

To ina godiya matuka da gaske Allah Ya bar zumunci Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply