Home Sabon Labari Taskar Guibi: Takaitattun Labarai da Sharhi 24.11.2019

Taskar Guibi: Takaitattun Labarai da Sharhi 24.11.2019

70
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, ashirin da shida ga watan Rabiul/Rabiyul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da hudu ga Nuwamba, na 2019.

1. Hukumar sojan saman Nijeriya ta yaba wa masakar da ke Zariya, da alkawarin masakar ce za ta dinga yi wa sojojin tanti, da falmaran da harsashi ba ya iya huda shi, da tamfal, da sauran muhimman kayayyaki na soja da suka jibanci kaki/tufa/yadi.

2. Wasu sun kai hari kauyen Shira-Kala, da ke yankin karamar hukumar Hong, da ke jihar Adamawa, suka kashe mutane.

3. Wani bincike ya nuna a halin yanzun haka, ‘yan Nijeriya su miliyan goma sha tara, ke fama da lalurar tsananin ciwon hanta da ke da hadarin gaske wato CHRONIC HEPATITIS.

4. Gwamnan jihar Zamfara Matawalle, ya zargi Abdul Aziz Yari da ta da zaune tsaye a jihar, a duk lokacin da ya je jihar, da gargadin idan ya kara ba zai kyale shi ba.

5. Amurka na zargin mamallakin kamfanin jiragen saman nan na AIR PEACE da ya taimaka ya dinga kwaso ‘yan Nijeriya kyauta a lokacin da ake ta kai musu harin kyama a Afirka ta Kudu, har aka masa alkawarin lambar yabo ta kasa, Mista Allen Onyema, da damfara ta banki, ta dala miliyan ashirin. Ya ce zargin ba shi da tushe domin duk wani abu da zai sayo a Amurka, ta hannun babban bankin Nijeriya yake aikewa da kudaden.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply