Home Sabon Labari Taskar Guibi: Takaitattun Labarai na 23.11.2019

Taskar Guibi: Takaitattun Labarai na 23.11.2019

104
0

Assalamu alaikum barkannu da asubahin asabar, ashirin da biyar ga watan Rabiul/Rabiyul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da uku ga watan Nuwamba, na shekarar 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wa ‘yan Nijeriya su sha kuruminsu, domin ba zai nemi tazarce zuwa wa’adi na uku da zaran ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu ba. Ya jaddada haka ne a wajen taron majalisar zartaswa/koli ta jam’iyyar APC.

2. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa hukumomin tsaro umarnin su kawo karshen ‘yan bindiga da kidinafas da ke ci gaba da addabar kasar nan. Sai dai wasu na korafin umarnin nasa da ya zama kullum sai ya yi sabo, ya isa haka nan, lokaci ya yi da zai tarkata manyan hafsoshin tsaro na kasar nan, ya saukar da su, ya sa sabbi.

3. Sojojin sama na Nijeriya sun soma gyara jiragensu na yaki da ake kira ALPHA JETS su da kansu a nan gida Nijeriya.

4. Sowore ya kai hukumar DSS kara kotu saboda ci gaba da tsare shi, da kuma bata masa suna, yana bukatar ta biya shi naira miliyan dari biyar.

5. Kotuna sun tabbatar wa da Ganduje da Tambuwal kujerun da suke kai na gwamna, tare da watsi da korafin masu kalubalantar zabensu.

6. Hukumar kula da kiyaye hadurra ta kasa FRSC ta kori wasu jami’anta su sittin da biyu, tana kuma kan bincikar wasu dari da saba’in da biyu da ake zargin suna karbar na goro. Har ila yau hukumar ta roki kamfanin da ke aikin Kaduna zuwa Zariya, ya bude turbar da ya kammala aikinta, don samun saukin haduran da suke ci gaba da aukuwa sakamakon mayar da yawancin hanyar zuwa hannu daya wato wanwe.

7. Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da hakimin yankin Gumi a kan mugun harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Karaye da ke yankin Gumin suka kashe mutane da dama da kona gidaje. Har ilau hukumar ‘yan sandan jihar ta hana lodin shanu a mota da daddare a jihar.

8. Gwamnatin jihar Kaduna ta soma rushe wasu gidaje ko gine-gine da ke cikin birnin jihar da take zargin an gina su ba ka’ida.

9. ‘Yan kungiyar Boko Haram su guda dari biyar da tamanin da suka tuba, suka isa Gwambe, don tsarkake musu zuciyarsu.

10. Sanata Dino Melaye, ya je shalkwatar hukumar zabe ta kasa INEC da bidiyo har guda ashirin da daya, da ke nuna yadda aka yi magudin zabe, a zabensu na Sanata da za a sake a wasu yankunan mazabarsa ranar talatin ga watan nan na Nuwamba.

 

Af! Ina ministan sadarwa Pantami? To talakawa na korafin kamfanonin sadarwa ba su bi umarni ko wa’adin da ka ba su na kwana biyar, ko su daina cutar talakawa bangaren DATA, ko ka sanya kafar wando guda da su ba.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply