Home Sabon Labari Taskar Guibi: Takaitattun Labaran 25.11.2019

Taskar Guibi: Takaitattun Labaran 25.11.2019

64
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, tushen aiki ko nasara yana tsoronki, ashirin da bakwai ga watan Rabiul/Rabiyul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da biyar ga Nuwamba, na 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa Salome Abuh wata jigon jam’iyyar PDP a ranar asabar 18 ga wannan watan, lokacin zaben gwamnan jihar Kogi, da ake zargin wasu matasan APC sun bi wani, ya fada gidanta, suka sa wa gidan nata wuta ta kone a ciki. Shugaban kasa ya ce dole sai an kamo wadanda suka kashe ta, kuma a hukunta su. Bayanai na nuna an kama wanda ya yi jagora zuwa kona gidan nata.

2. Gwamnatin tarayya za ta hana shigo da bakin karfe da danginsa kasar nan.

3. Sanata Abdullahi Sebi wanda shi ne makikkirin kudirin dokar nan ta hukuncin kisa ga wanda ya yi kalaman kiyayya a soshiyal midiya, ya ce zai cire shedarar ta hudu, dan karamin sashe na biyu, da ya yi tanadin kisa a cikin kudirin, saboda sukar da yake ta sha a kan wannan kudirin doka na HATE SPEECH.

4. Gwamnatin tarayya za ta dasa itatuwa guda miliyan ashirin da biyar domin magance matsalar sauyin yanayi.

5. Wata kotun Amurka ta ba da warantin a kamo mata Allen Onyema, shugaban kamfanin Air Peace, da take tuhumarsa da laifuka har guda ashirin da bakwai.

6. Babban hafsan tsaro na kasar nan janar Gabriel Abayomi, na rangadin makarantun firamare da sakandare domin cusa wa yara ‘yan makaranta, kaunar aikin soja.

7. Kan kungiyar malaman jami’o’i ASUU ya rabu gida biyu, a kan yarda a sa su cikin tsarin nan na IPPIS.

8. Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba, ya ba da umarnin kawo karshen rikicin al’umar kauyen Kwararrafa.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Kwana biyu ban yi magana a kan wutar lantarki ba. Har na tuna tsokacin da wani ya mun a daya daga cikin rubuce-rubucen da na yi a makon shekaranjiya. Ya ce “Guibi idan ka sake damunmu da zancen ba wuta, to ka isa bakauye”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply