Home Sabon Labari Taskar Guibi: Takaitattun Labaran 29.12.2019

Taskar Guibi: Takaitattun Labaran 29.12.2019

82
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, biyu ga watan Jimada Auwal/Ula, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da tara ga watan Disamba, shekarar 2019.

1. Sojoji da ‘yan sanda sun dakile wasu ‘yan fashi da suka shiga wani banki na First Bank da ke Abuja don aikata fashin, aka kama hudu aka bindige daya ya mutu. Daya daga cikin wadanda aka kama ya ce da hadin bakin manajan bankin suka je fashin.

2. Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Abdulsalam Abubakar sun sa baki don sasanta gwamnan Kano Ganduje da Sarkin Kano Sanusi na biyu.

3. Za a gina sakatariyar jihar Kwara a filin da aka kwace a hannun Bukola Saraki.

4. Cif Obasanjo ya ce abin da ke ci wa kasar nan tuwo a kwarya a yanzun, shi ne yadda aka dankara mata bashin da ya fi karfinta.

5. Majalisar Dattawa ta ce za ta amince da kudirin dokar gyaran zabe a shekarar 2020 da ke shirin kankama.

6. Hukumar kiyaye hadurra na nan tana gwajin direbobi don gano direbobin da ke kwankwadar barasa kafin su hau hanya.

7. Kidinafas na ci gaba da damun unguwar Ketti da ke yankin Abuja inda suke ta satar musu jama’a.

8. Hakimin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna da kidinafas suka karbi makudan kudi don su sako shi, a karshe suka ki sako shi ya samu ya kubuce daga hannunsu ya koma gida.

9. Ma’aikatan gwamnatin tarayya na ci gaba da dakon ariyas na sabon albashi da gwamnatin tarayya ta musu alkawarin za a biya su kafin karshen wannan watan. Yau dai ashirin da tara ga watan da ke nuna saura kwana biyu watan ya kare. Tambayar da wasunsu ke yi ita ce anya za a iya biyansu cikin kwana biyun da ya yi saura ko za a saba alkawari sai an shiga sabuwar shekara? Tun dai a watan Afrilun shekarar nan aka yi karin sabon albashin, da wasu ma’aikatan har zuwa yau ba su shaida ba, wasu sun shaida a albashin wannan watan sai dai sun yi korafin karin bai wuce na naira dubu uku ba, da dai sauran korafe-korafe.

10. Wasu na nan suna korafin sanyin bana kam sai a hankali.

11. Akwai dai zawarawa a kasa in akwai mai muradi.

 

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply