Home Taskar Guibi Taskar Guibi:22.06.2020

Taskar Guibi:22.06.2020

263
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, ko dai talatin ga watan Shawwal ko daya ga watan Zulkida shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyu ga watan Yuni, na shekarar dubu biyu da ashirin.

Na ce talatin ga watan Shawwal ko daya ga watan Zulkida ne saboda har wuraren karfe biyun dare da na kwanta bacci ban ji labarin ganin jinjirin watan Zulkida ba.

1. Duk da bacin ran da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna wa manyan shugabannin bangarorin tsaro na kasar nan, ‘yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare kauyukan Arewa. Shekaranjiya Asabar da yamma suka auka Ruwan Tofa da ke yankin Dan Sadau a jihar Zamfara da babura da bindigogi, suka kashe na kashewa, suka jikkata na jikkatawa. Sannan kafin wannan rana wasu ‘yan bindigan sun kai hari yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina, suka kashe mutum a kalla bakwai.

2. Sojojin sama sun ce sun kai hari dajin Sambisa da ke jihar Barno, a cikin abubuwan da suka lalata har da wata mota mai bindigar kakkabo jiragen sama na yaki. Suka ce an ma harbi jirginsu na yaki, ya kauce, sannan ya tarwatsa motar.

3. Likitocin nan da suka dilmiya yajin aiki saboda wasu alawus-alawus dinsu, sun janye yajin aikin bayan sun ga cewa da gaske gwamnatin tarayya ta ba da kudi a biya su.

4. Mataimakin gwamnan jihar Ondo Agboola ya fice daga jam’iyyar APC ya koma PDP. Har ma da yake kokarin ficewa daga gidan gwamnati kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya tare shi cewa ba zai fita ba. Har mataimakin gwamnan ke tambayar kwanishinan ‘yan sandan ko shi ne shugaban jam’iyyar APC har da zai hana shi fita? Daga bisani gwamnan jihar ya nesanta kansa da abin da aka yi zargin kwamishinan ya yi wa mataimakin gwamnan.

5. Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun rusa ginin da ma’aikatan babban ofishin jakadanci na Nijeriya da ke Ghana ke zama a ciki, da ke harabar babban ofishin jakandaci na Nijeriya a Accra Ghana. Gwamnatin Ghana ta nemi gafara daga Nijeriya da alkawarin yau litinin za su leka wajen don tantance me ya faru. Gwamnatin Nijeriya ta nuna matukar bacin ranta a kai. Da ma an ce akwai ‘yar wata takaddana a kan ginin.

6. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata biyu har da wasu kwanaki suna zaman jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

7. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 436 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 169
Oyo 52
Plateau 31
Kaduna 28
Imo 29
Ogun 23
Abuja 18
Inugu 18
Bauci 17
Bayelsa 14
Ribas 8
Oshun 6
Kano 6
Edo 5
Binuwai 5
Adamawa 3
Barno 2
Abiya 1
Ekiti 1

Wadanda suka harbu zuwa jiya su dubu ashirin, da dari biyu da arba”in da hudu. Wadanda suka warke su dubu shida, da dari takwas da saba’in da tara. Sai mutum dari biyar da goma sha takwas da ya riga mu gidan gaskiya. Sai mutum dubu goma sha biyu, da dari takwas da arba’in da bakwai da ke jinya.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Gaisuwa da godiya ta musamman ga limamin Barnawa da ke cikin garin Kaduna Malam Murtala Yusuf. Ina godiya da bibiyata kullum da asubah, da kuma sanya ni da kake yi cikin addu’a a kullum. Ina godiya kwarai da gaske Allah Ya saka, Ya ci gaba da tsare mu da tsarewarSa daga dukkan sharri da masharranta na fili da na boye Amin.
Ga bayanin da Malam Murtala limamin na Barnawa ya turo :

“Wslm, kwarai kuwa Dr. nine Wanda muka taba gaisawa dakai a can ABU Zaria, hakika Dr. muna karuwa da kake wallafawa kullum a shafinnan naka mai albarka Wallahi kullum sai na karanta labarun da kake wallafawa nake samun natsuwa. Muna fatan Allah ya kara basira ya Kuma kiyaye mana Kai daga sharrin makiya na boye dana bayyane”

Haka nan ina godiya ga dukkan wadanda suke ci gaba da mun addu’a.

Yanzun karfe hudu da minti ashirin da biyar na asubah ruwan sama ya sauko.

  1. Is’haq Idris Guibi
    Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply