Home Taskar Guibi Taskar Guibi:25.06.2020

Taskar Guibi:25.06.2020

303
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, uku ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyar ga watan Yunin shekarar 2020.

1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya raba gardama ya goya wa Giadom baya a matsayin shugaban APC na kasa na riko, har ga Giadom din ma ya kira taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar yau a fadar shugaban kasa, kuma shugaban kasa Buhari zai halarci taron. Wannan goya baya da ya yi wa Giadom koma baya ce ga Oshiomhole da Tinubu. Kuma da ma Giadom ya aike wa hukumar zabe cewa ba a yi zaben fid-da-gwani na wanda zai tsaya wa jam’iyyar ta APC takarar gwamnan jihar Edo ba.

2. An daidaita a wajen kotu, gwamna Obaseki zai shiga takarar fid-da-gwani na ‘yan takaran PDP, don fitar da wanda zai tsaya wa PDP takarar gwamna na jihar Edo.

3. Babban Bankin Duniya ya amince ya ba Nijeriya bashin dala miliyan dari bakwai da hamsin da ta nema domin gyaran bangaren wutar lantarki.

4. Rundunar tsaro ta Amotekun ta kama shanu guda arba’in da biyu da take zargin sun yi barna a gonaki a Akure.

5. A jihar Nasarawa jami’an tsaro sun kama wanda ya yi wa jaririya ‘yar wata uku fyade, haka nan a jihar Kabbi ma an kama wasu da ke yi wa yara fyade, da jihar Akwa Ibom da aka kama wani fasto yana yi wa yara ‘yan mata fyade da sunan rukiyya.

6. Sojojin sama sun ce sun kai hare-hare dazuzzukan da makasa suke a jihar Katsina da ta Zamfara.

7. Gwamnatin Tarayya ta aike wa Majalisar Dokoki ta Kasa tsarin bude makarantu da aka rufe saboda kwaronabairos.

8. Gwamnatin Ghana ta ce ta kama mutum biyu da ke da hannu a rushe ginin da ke ofishin jakadanci na Nijeriya da ke Accra Ghana, kuma za a gurfanar da su gaban kuliya.

9. An soma yi wa ‘yan majalisar dokoki ta jihar Kaduna gwajin kwaronabairos saboda gano wani ma’aikacin majalisar yana da cutar.

10. ‘Yan sanda sun kama wasu daga cikin shugabannin kanfanin shinkafa da ke Kano wato Popular Rice Mill saboda rufe ma’aikatan kamfanin a ciki har tsawon wata uku ba shiga ba fita suna aiki, su wajen dari uku, tsoron kada su fita su dauko cutar kwaronabairos cikin kamfanin.

11. Yau za a kwaso ‘yan Nijeriya su dari biyu daga Afirka ta Kudu zuwa gida.

12. ‘Yan sanda sun kama wasu mata uku da harsashi guda dari takwas da goma sha takwas boye cikin shinkafa a buhu, sun dauko daga Kano za su kai jihar Bayelsa.

13. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik na gwamnatin tarayya, da na kwalejojin ilimi na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya, da kusan wata uku ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

14. Jiya kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 649 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 250
Oyo 100
Filato 40
Abiya 28
Kaduna 27
Ogun 22
Edo 20
Akwa Ibom 18
Kwara 17
Abuja 17
Inugu 14
Neja 13
Adamawa 13
Bayelsa 7
Oshun 6
Bauci 6
Anambra 4
Gwambe 3
Sakkwato 2
Imo 1
Kano 1

Zuwa jiyan mutum dubu ashirin da biyu da guda ashirin ya harbu da kwaronabairos a kasar nan, sai mutum dubu bakwai da dari shida da goma sha uku da ya warke, sai mutum dari biyar da arba’in da biyu da ya riga mu gidan gaskiya. Sai mutum dubu goma sha uku, da dari takwas da sittin da biyar da ke jinya.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Yau fa ashirin da biyar ga watan Yuni, ya kamata a ce an soma jin duriyar dilin-dilin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply