Home Sabon Labari TASKAR GUIBI>Karanta Takaitattun Labarai da Sharhi 28.10.2019

TASKAR GUIBI>Karanta Takaitattun Labarai da Sharhi 28.10.2019

80
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, ashirin da tara ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da takwas ga Oktoban 2019.

1. Yau shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi Saudiya don halartar wani taro da ya shafi zuba jari. Ga wani can yana cewa “saura kuma in ji wani ya kara cewa yawale sai na yawale shi ya yi tuntsira gudigudi sau arba’in da bakwai” Ga wani can yana cewa ai ko tafiyarsa kasashen duniya ta arba’in da bakwai ke nan da hawansa mulki. Ga wani can yana ce masa “kai kuwa maimakon ka tsaya kana lissafin yau watakila watan Safar ya kare a ga sabon jinjirin watan haihuwar manzon Allah, ka takarkare kana lissafin sau nawa Baba Buhari ya fice kasar? Ba ka ji bankin duniya ya ce Nijeriya ta fara yi wa sauran kasashen duniya fintinkau bangaren walwalar kasuwanci da bunkasar tattalin arziki ba ne? Ko kana da ja ne? Zauna nan ka zama kifin rijiya. Da sassafe ake kama fara, idan rana ta yi sai su watse.”

2. A ranar ashirin da takwas da kuma talatin duk ga wannan watan kotun koli za ta saurari daukaka karar da Atiku Abubakar zai yi, ta kalubalantar zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari. Hmm bakina da goro.

3. Sojojin sama za su yi wani atisaye na tauna tsakuwa don firgita aya ta ji tsoro a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, saboda haka ake rokon jama’a idan sun ji rugugin bindiga da amon kayan yaki ta sama da kasa, kada su firgita ko aukawa cikin wata fargaba, su ci gaba da gudanar da sabgoginsu. Ga wani can na cewa soja birgimar hankaka. Kowa ya ga bakinku ya ga farinku.

4. ‘Yan sanda sun yi nasarar kwato shanu guda talatin da shida daga hannun barayin shanu a jihar Zamfara. Ga wani can yana tambayar ko an soma samun kidinafas na shaniu ne? Shi dai ya san a Kaduna an taba kidinafin wani kare sai da aka biya kudin fansa lakadan aka sako shi.

5. Ambaliya ta yi sanadiyyar raba al’umomi da dama da muhallansu a jihar Adamawa da ta Taraba. Ga wani can yana cewa a Kaduna ma wasu sun soma rokon Allah Ya kawo saukin yawan ruwan saman da ake ta samu saboda kada amfanin gona irin su dawa da ke bukatar ban iska su lalace a shiga wani yanayi na rashin abinci.

Mu wayi gari lafiya.

 

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply