Home Sabon Labari Taskar Guibi: Yau Take Sallah 11.08.2019

Taskar Guibi: Yau Take Sallah 11.08.2019

55
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, goma ga watan Zulhijja/Zulhajj, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha daya ga Agustan 2019.

Yau take babbar Sallah wato sallar layya ko Idil-Kabir. Da ake kame baki kafin a je Idi, da kabarbari/takbir a hanyar zuwa masallaci, da canza hanya idan za a dawo, da kuma yanka abin da Allah Ya hore ko huwace wa mutum na layya, bayan liman ya yanka nasa, bayan an idar da Sallah, ya kammala huduba. Allah Ya sada mu da dinbin lada da falalar da ke ciki Allah Ya sa mu cika da kyau da imani, Ya mana maganin masifa, Ya jikan iyayenmu da kakanninmu, Ya rufa mana asiri duniya da lahira. Ya raba mu da asara, Ya mana katangar karfe da kidinafas, da makasa, da mahassada, da makiya, da tsautsayi da talauci da kunci. Ya raba mu da iyayenmu lafiya, Ya ba mu zuri’a ta gari, in za mu cika, Ya sa mu cika da kyau da imani, kada mu wulakanta ko tozarta ko mutuwa ta wulakanci. Allah Ya biya wa kowa bukatarsa ta alheri.

Is’haq Idris Guibi dan jarida kuma mai sharhi a Kaduna

Mai neman haihuwa ko miji ko mata ko aiki ko karatu ko gida ko rufin asiri da sauran ci gaba, Allah Ka masa. Allah Kai ne Allah Ka yi Allan naKa kamar yadda Ka saba, Ka isar mana ga duk wani azzalumi, macuci. Allah Ka sa aljanna ta zama makomarmu. Allah mun tuba, Ka yafe mana kurakuranmu da muka aikata a sarari ko a boye, da saninmu ko ba da saninmu ba, Ka dawo mana da alhazanmu lafiya, Ka karbi hajjinsu da addu’o’insu, su kuma shugabanni Ka ba su ikon yi mana adalci da dora su bisa turba ta gari. Ka raba mu da mugun ji da mugun gani. Mugun mutum ko aljan na sarari da na boye Allah Kai Ka sansu Ka mana maganinsu. Allah Ka tsarkake mana imaninmu da zuciyarmu da dukiyarmu ka ciyar da mu da halas ba haram ba Amin.

Mu yi shagulgulan Sallah lafiya.

Af! ‘Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari al’umar Gubio da ke jihar Barno.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply