Home Sabon Labari Taskar Guibi: Karya kumallo da takaitattun labarai

Taskar Guibi: Karya kumallo da takaitattun labarai

80
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, goma sha uku ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha biyu ga Oktoba, na 2019.

  1. Babban labarin da ya cika soshiyal midiya, da gidaje, da unguwanni, da kasuwanni, da ma’aikatu, da sauran wuraren mu’amala ta jama’a shi ne jiya shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi wa Aisha kishiya. Wadanda suka kitsa labarin ko taya bera bari ko buruntu har da zama su tsara katin auren, da waje da lokaci, wasu hada hotuna, wasu bidiyo. Ni dai ko a rubutuna na jiya da asubah na sa ban yarda da labarin ba. Tunda in har shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi aure da gaske, akwai mukarrabansa da dole ka ji daga bakinsu ta hanyoyi daban-daban. Wannan ke kara fito da hadarin da ke tattare da yada labarin kanzon kurege ko jitajita a soshiyal midiya. Har fa jiya da daddare mutanen da nake tare da su ba mazan ba, ba matan ba, na ce mun an daura auren shugaban kasa.
  2. Gwamnatin tarayya ta dan dakatar da manyan mukarraban gwamnati daga tafiya kasashen waje, don su samu damar zuwa kare kasafinsu a majalisar dokoki ta kasa a yi a gama kasafin 2020 cikin hanzari.
  3. Kamfanin mai na kasa NNPC ya ce an gano mai da sauran wasu ma’adinai a yankin Gwangola/Gongola.
  4. Sojojin kundinbala na THUNDER STORM sun ceto ‘yan makarantan nan shida da kidinafas suka yi kidinafin a Kaduna.
  5. Kotu ta yi fatali da daukaka karar da Sanata Dino Melaye ya yi a kan hukuncin da kotun kararrakin zaben sanata ta yanke tun farko na soke zabensa. Kotun ta ba da umarnin gudanar da sabon zabe a mazabar tasa nan da kwana casa’in.
  6. Hukumar EFCC ta mika wa gwamnatin jihar Kwara wata naira miliyan dari da goma sha daya da ta ce ta kwato daga hannun wasu rikakkun gafiyoyi da suka wawushe dukiyar jiyar.
  7. Mataimakin shugaban kasa Osinbanjo ya ce babu wata kasar Afirka da ba a aikata rashawa a cikinta.
  8. Masu fitar da kayayyakin Nijeriya zuwa kasashen ketare sun ce rufe bodojin kasar nan da aka yi ta sa cinikinsu ya ja baya.
  9. Sojoji sun murkushe wasu ‘yan kungiyar Boko Haram su wajen goma sha biyar a jihar Barno.
  10. Kotu ta ba EFCC umarnin ta tsare Abdulrasheed Maina da dansa.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Me ma na tuna?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply