Home Coronavirus Tattalin arziƙin Nijeriya na dab da rushewa

Tattalin arziƙin Nijeriya na dab da rushewa

137
0

Ministan kudi, kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmed ta ce tattalin arzikin Nijeriya na dab da durkushewa.

Saidai ta ce za a iya takaita illar durkushewar tattalin arzikin, idan har an aiwatar da tsare-tsaren karfafa tattalin arzikin.

Ministar ta shadaiwa ‘yan jarida a Abuja cewa, cutar Covid-19 ta yi illa ga farashin danyen mai, kuma hakan tuni ya fara nunawa ga kudaden shigar gwamnatin tarayya da kuma kasuwar musayar kudaden waje.

Ta kara da cewa bankin duniya, ya yi tayin tallafin Dala Biliyan daya da rabi ga jihohi domin rage illar da cutar ta haifar.

Ta kuma yi hasashen cewa ko wace jiha za ta samu Naira Biliyan 150 zuwa 200.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply