Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Tattalin arziƙin Nijeriya ya bunƙasa ta hanyar kasuwanci – Rahoto

Tattalin arziƙin Nijeriya ya bunƙasa ta hanyar kasuwanci – Rahoto

151
0

Wani rahoto da Banki Duniya ya fitar kan sauƙaƙa harkokin kasuwanci, ya sanya Nijeriya daga cikin jerin ƙasashen duniya 10 da tattalin arziƙinsu ya bunƙasa ta hanyar kasuwanci.

Kafin fitar da wannan rahoto bankin Duniyar sai da ya bi diddigin harkokin kasuwanci da ma yadda ake gudanar da su a ƙasashen Duniya 190.

Nijeriya dai ta shiga cikin jerin ƙasashen da suka samu ci gaba a fannin harkokin kasuwanci da suka haɗa China, Saudiya, Jordan, Bahrain Pakistan, Indiya, Kuwait da dai sauran su.

Sai dai rahoton ya ce ƙasashen ba su kai ga cin nasara ba sai da su ka aiwatar da sabbin tsare-tsare guda 55 na tsarin kasuwancin zamani.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply