Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ta hanyar inganta hakar ma’adanai zai kara samar ayyukan yi ga al’ummar Nijeriya kusan dubu dari biyu da hamsin, dama samar wa kasa da kudaden shiga da sukai dala bilyan dari biyar.
Buhari ya bayyana hakan ne ya yin da ya ke kaddamar da wani zinare da aka sarrafa a nan Nijeriya karkashin shirin nan haka da bunkasa shirin ma’adanai.
