Home Labarai Tattaunawar ASUU da gwamnati za ta ci gaba ranar Juma’a

Tattaunawar ASUU da gwamnati za ta ci gaba ranar Juma’a

93
0

Gwamnatin tarayya ta ce za ta ci gaba da ganawa da ƙungiyar malaman jami’o’i ASUU a ranar Juma’a.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Ƙwadago Charles Akpan ya bayyana haka a wani saƙo da ya aike a daren Laraba.

Ana sa ran taron dai zai warware batutuwa da dama tsakanin gwamnati da ƙungiyar ciki har da tsarin biyan kuɗi da ake ta kai ruwa rana kansa tsakanin ɓangarorin biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply