DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 10, 2026
HomeSiyasaTinubu ba cire tallafin man fetur ya yi ba, abokansa masu ƙuɗi...

Tinubu ba cire tallafin man fetur ya yi ba, abokansa masu ƙuɗi ya bai wa dama – Zargin Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da cewa ikirarin cire tallafin man fetur bai dace da yadda take bai wa manyan masu zuba jari a fannin mai rangwamen haraji da wasu sauƙaƙan tsare-tsare ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Lahadi, Atiku ya ce gwamnati ta ɗora wa talakawan Nijeriya nauyin tsadar man fetur, sufuri da rayuwa, yayin da kuma take samar da rangwame da tallafin kasafin kuɗi ga manyan kamfanonin mai.

Ya ce bayanan kuɗin NNPCL na shekarun 2023 da 2024 sun nuna biliyoyin Naira da aka kashe a matsayin kuɗaɗen tsaron makamashi da sauran gibin farashi, yana mai tambayar yadda za a ce an cire tallafin man fetur alhali gwamnati na ci gaba da ɗaukar nauyin wasu bambance-bambancen farashin.

Atiku ya jaddada cewa shirin farfaɗo da tattalin arzikin da ya gabatar ba yana nufin dawo da tsohon tsarin tallafin man fetur mai cike da almundahana ba ne, sai dai samar da tallafi na musamman ga masu rauni, cikin tsari, a wuraren da suka dace.

A cewarsa, bai dace gwamnati ta ɗauki tallafawa manyan masu zuba jari a matsayin kyakkyawar manufar tattalin arziki ba.

Saidai sanarwar ta yi watsi da duk wani shiri na rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa, da gwamnatin ta Tinubu ta ce ta na yi.

“Atiku ba zai daina fafutukar dawo da tallafi na musamman ga ‘yan Nijeriya masu fama da tsadar rayuwa ba, ko da mutum miliyan 100 masu suna Tinubu za su yi ƙoƙarin hana shi,” in ji sanarwar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata