Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar PRP, Donald Duke, ya bayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin gogaggen ɗan siyasa mai ƙarfi, yana mai gargaɗin ’yan adawa cewa ba za su iya kayar da shi a zaɓen 2027 ba matuƙar ba su haɗa kai ba.
Tsohon gwamnan jihar Cross River ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a ranar Juma’a.
Duke ya ce duk wani yunƙurin ’yan adawa na kalubalantar jam’iyyar APC da Tinubu ba tare da samar da haɗin kai tsakanin jam’iyyun adawa ba, zai iya ƙara wa shugaban ƙasar damar samun nasara.
Ya ce bai kamata ’yan adawa su raina ƙarfin Tinubu a kan kujerar shugaban ƙasa ba, domin kasancewar jam’iyya mai mulki na ba ta damar amfani da cibiyoyin gwamnati wajen gudanar da zaɓe.
Duke ya bayyana cewa idan wata matsala ta taso a ranar zaɓe, jami’an gwamnati irin su Sufeto-Janar na ’yan sanda za su karkata zuwa ga shugaban ƙasa, wanda hakan ke nuna irin fa’idar shugaba mai ci da mulki ke da ita.
A cewarsa, wannan yanayin ya sa ya zama wajibi ’yan adawa su haɗa kai idan da gaske suke son ƙalubalantar Tinubu a 2027.
Ya ce rashin haɗin kan ’yan adawa na iya zama tamkar suna cin nasara a kansu da kansu, saboda son zuciya da burin kowane ɗan siyasa na ganin ya samu matsayi.
Ya ce Tinubu “ba ƙaramin ɗan siyasa ba ne”, don haka duk wanda ke son ƙalubalantar sa dole ne ya fahimci irin ƙarfin siyasar da yake da shi tare da shirya dabarun da suka dace.
Tsohon gwamnan ya ƙara jaddada cewa ’yan adawa na bukatar su ajiye wasu daga cikin burinsu da bambance-bambancen kansu domin gina wani babbar ƙawance da zai iya fafatawa da APC a zaɓen 2027.
Ya ce rarrabuwar kawuna tsakanin ’yan siyasa na iya amfani ne kawai ga jam’iyya mai mulki, yayin da haɗin kai zai ba ’yan adawa damar samar da ingantacciyar gwamnati.
Duke, wanda shi ne ɗan takarar PRP a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, na daga cikin ’yan siyasar adawa da ke neman kalubalantar Tinubu da APC a babban zaɓen da ke tafe.
Kalaman nasa sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa da yunƙurin ƙulla ƙawancen ’yan adawa domin samar da wata babbar rundunar siyasa da za ta iya fuskantar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
