DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeBabban Labari Tinubu ya ƙuduri aniyar farfado da matatun man Nijeriya duk da shakkun...

Tinubu ya ƙuduri aniyar farfado da matatun man Nijeriya duk da shakkun da Obasanjo ya ke

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce matatun man fetur na Fatakwal da Warri za su dawo aiki gadan-gadan, duk da shakkun da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya nuna kan yiwuwar samun nasarar farfaɗo da su.

Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi bakuncin shugaban ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta ƙasa, NUPENG, Salimon Oladiti, da sauran shugabannin ƙungiyar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Shugaban ya ce gwamnatinsa ba za ta tsaya kan abin da ya faru a baya ba, yana mai cewa ya karɓi dukkan kadarori da nauyin da gwamnatocin baya suka bari, kuma alhakin sa ne ya tabbatar da cewa matatun sun fara aiki yadda ya kamata.

Jaridar Punch ta kuma ruwaito Tinubu ya jaddada cewa muradinsa shi ne tabbatar da ganin matatun suna aiki yadda ya kamata kuma suna samar da riba ga tattalin arzikin kasar.

Sai dai wannan matsaya ta Tinubu ta bambanta da ra’ayin Obasanjo, wanda ya dade yana ganin cewa kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC, ba shi da damar gudanar da matatun gwamnatin cikin nasara.

Obasanjo ya ce ya fi ganin ya dace a bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar gudanar da matatun, yana mai cewa tsarin haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, PPP, ya fi dacewa wajen gudanar da manyan kadarorin ƙasar.

Tsohon shugaban ya bayyana cewa lokacin da yake shugaban ƙasa tsakanin 1999 zuwa 2007, ya yi ƙoƙarin bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar gudanar da matatun. Ya ce ya nemi Shell ta mallaki kashi 10 cikin 100 tare da gudanar da su, amma kamfanin ya ƙi.

Obasanjo ya ce daga baya ya nemi Shell ta gudanar da matatun ba tare da ta mallaki wani kaso ba, amma kamfanin ya sake ƙin amincewa da hakan.

A cewarsa, Shell ta bayyana cewa girman matatun, rashin kulawa da su, da kuma matsalolin cin hanci da rashawa na daga cikin dalilan da suka sa ba ta son shiga harkar.

Ya kuma tuna cewa hamshakin ɗan kasuwa Aliko Dangote ya taba bayar da dala miliyan 750 domin mallakar kaso 51 cikin 100 na wasu matatun biyu, amma daga baya aka soke yarjejeniyar bayan ya bar mulki.

Obasanjo ya ce ya yi gargadi a lokacin cewa NNPC ba za ta iya gudanar da matatun yadda ya kamata ba, yana mai cewa soke yarjejeniyar na iya jawo asarar wata muhimmiyar dama ga ƙasar.

Haka kuma, ya yi iƙirarin cewa gwamnati ta narka kusan dala biliyan 16 wajen ƙoƙarin gyara matatun, adadin da yake ganin ya yi matuƙar yawa idan aka kwatanta da kuɗin da aka ɓatar wajen gina matatar Dangote.

Sai dai masu sayar da man fetur a yankin da ke yankin matatar ta Fatakwal sun goyi bayan ƙudurin Tinubu na farfaɗo da matatar.

Tinubu ya ƙuduri aniyar farfado da matatun man Nijeriya duk da shakkun da Obasanjo ya ke

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce matatun man fetur na Fatakwal da Warri za su dawo aiki gadan-gadan, duk da shakkun da tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo ya nuna kan yiwuwar samun nasarar farfaɗo da su.

Tinubu ya jaddada hakan ne a lokacin da ya karɓi bakuncin ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta ƙasa, NUPENG, da shugabanta Salimon Oladiti ya jagoranta a Abuja.

Shugaban ya ce gwamnatinsa ba za ta tsaya kan abin da ya faru a baya ba, yana mai cewa ya karɓi dukkan kadarori da nauyin da gwamnatocin baya suka bari, kuma alhakin sa ne ya tabbatar da cewa matatun sun fara aiki yadda ya kamata.

Jaridar Punch ta ruwaito Tinubu ya na kuna tabbatar muradinsa na ganin matatun suna samar da riba ga tattalin arzikin kasar.

Sai dai wannan matsaya ta Tinubu ta bambanta da ra’ayin Obasanjo, wanda ya dade yana ganin cewa kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ba shi da damar gudanar da matatun gwamnatin cikin nasara.

Obasanjo ya ce ya fi ganin ya dace a bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar gudanar da matatun, tare da cewa tsarin haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, PPP, shi ya fi dacewa wajen gudanar da manyan kadarorin ƙasar.

Tsohon shugaban ya bayyana cewa lokacin da yake shugaban ƙasa tsakanin 1999 zuwa 2007, ya yi ƙoƙarin bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar gudanar da matatun. Ya ce ya nemi Shell ya mallaki kashi 10 cikin 100 tare da gudanar da su, amma kamfanin ya ƙi.

Obasanjo ya ce daga baya ya nemi Shell ya gudanar da matatun ba tare da ta mallaki wani kaso ba, amma kamfanin ya sake ƙin amincewa da hakan.

A cewarsa, Shell ya bayyana cewa girman matatun, rashin kulawa da su, da kuma matsalolin cin hanci da rashawa na daga cikin dalilan da suka sa ba ya son shiga harkar.

Ya kuma tuna cewa hamshakin ɗan kasuwa Aliko Dangote ya taba bayar da dala miliyan 750 domin mallakar kaso 51 cikin 100 na wasu matatun biyu, amma daga baya aka soke yarjejeniyar bayan ya bar mulki.

Obasanjo ya ce ya yi gargadi a lokacin cewa NNPC ba zai iya gudanar da matatun yadda ya kamata ba, yana mai cewa soke yarjejeniyar na iya jawo asarar wata muhimmiyar dama ga ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata