DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeBabban Labari Tinubu ya gaji tattalin arzikin Nijeriya cikin mawuyacin hali - Akpabio

Tinubu ya gaji tattalin arzikin Nijeriya cikin mawuyacin hali – Akpabio

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya ce gwamnatin shugaban Bola Ahmed Tinubu ta APC za ta samu gagarumin abin da za ta gabatar wa ‘yan Nijeriya yayin neman wa’adin mulki na biyu a babban zaɓen 2027.

Jaridar Punch ta ruwaito Akpabio ya ce Tinubu ya gaji tattalin arzikin ƙasar cikin mawuyacin hali lokacin da ya hau mulki a shekarar 2023, yana mai ikirarin cewa a wancan lokacin jihohi 27 ba su iya biyan albashin ma’aikatansu da kuma biyan fansho ba.

Ya bayyana hakan ne lokacin da kwamitin majalisar dattawa mai kula da manyan makarantu, TETFund da NELFund, ƙarƙashin jagorancin sanata Dandutse Mohammed, suka kai masa ziyarar girmamawa a gidansa da ke Uyo, jihar Akwa Ibom.

A cewarsa, sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun taimaka wajen sauya yanayin tattalin arzikin ƙasar, tare da cewa ‘yan Nijeriya za su tantance ayyukan gwamnati da na masu hamayya kafin yanke hukunci a zaɓen 2027.

Akpabio ya ce gwamnatin APC tana da manyan nasarori a fannoni da suka haɗa da tattalin arziki, noma, tsaro, ilimi da manufofin kuɗi, duk da cewa masu hamayya ba sa son amincewa da waɗannan nasarori saboda bambancin siyasa.

Ya kuma kare ayyukan majalisa ta 10, yana mai cewa ƙarƙashin jagorancinsa majalisar dattawa ta amince da dokoki da dama da aka tsara domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da haɗin gwiwa da bangaren zartarwa.

Shugaban majalisar dattawan ya kuma buƙaci ‘yan majalisar da ba za su koma majalisa ta 11 ba da su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga APC da gwamnatin Tinubu, yana mai tabbatar musu da cewa jam’iyya da shugaban ƙasa za su yaba da gudummawar da suka bayar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata