Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umurci wani kwamitin mutum 11 da ya kammala tantance manyan ƙalubalen tsaron ƙasar tare da tsara dabarun ayyukan tsaro na shekaru biyar cikin kwanaki 90.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Tinubu ya bayar da umarnin ne a yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar a fadar shugaban da ke Abuja ranar Laraba.
Kwamitin zai gudanar da cikakken bincike kan barazanar tsaron da Nijeriya ke fuskanta, tare da tsara hanyoyin da za a inganta haɗin gwiwa tsakanin rundunonin tsaro, hukumomin leƙen asiri da sauran hukumomin da abin ya shafa.
Kwamitin ya ƙunshi manyan jami’an tsaro da suka haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron cikin gida, da NSA, ministan tsaro, shugaban hafsoshin tsaro da shugabannin rundunonin sojojin ƙasa, sama da ruwa.
Shugaba Tinubu ya ce sabon tsarin zai taimaka wajen gano gibin da ake da shi wajen kayan aiki da ƙwarewa, tare da tsara abubuwan da ya kamata a fi bai wa muhimmanci wajen kare ƙasar.
An kuma bai wa kwamitin wa’adin kwanaki 90 domin gabatar da rahotonsa da kuma cikakken tsarin tsaro na shekaru biyar ga Shugaba Tinubu domin amincewa.
Tinubu ya ce da zarar an amince da tsarin, zai zama babban tsarin da za a riƙa amfani da shi wajen tsara da daidaita ayyukan sojoji da sauran hukumomin tsaro a matsakaicin lokaci.
