DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeSiyasaTinubu ya yi umarnin a gaggauta ceto mutanen da aka sace a...

Tinubu ya yi umarnin a gaggauta ceto mutanen da aka sace a masallaci a Neja

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci rundunar sojin kasar, ’yan sanda, hukumar tsaro ta DSS da sauran hukumomin tsaro da leƙen asiri su haɗa kai wajen gaggauta ceto mutanen da aka sace a wani mummunan hari da aka kai jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito maharan sun kai farmaki masallatai huɗu a ƙauyukan Dekara, Kpenya, Sabon-Gida da Gidan-Zana da ke ƙaramar hukumar Borgu a lokacin sallar Juma’a da ta gabata, inda suka yi awon gaba da ɗimbin masu ibada tare da hallaka wasu daga cikin mutanen yankin.

A cikin martaninsa, shugaban ya bayyana matuƙar fushinza kan harin, yana mai cewa waɗanda suka aikata wannan ta’asa maƙiyan zaman lafiya ne.

Inda aka ambato shi ya na jaddada cewa ba za su tsira daga hukunci ba, ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a farmakin.

Tinubu ya ce gwamnati ba za ta huta ba har sai an ceto dukkan waɗanda aka sace tare da dawo da su ga iyalansu cikin koshin lafiya.

Ya umarci hafsoshin tsaro su riƙa ba shi rahoto akai-akai kan yadda aikin ceto ke gudana har sai an gano makomar kowane mutum da aka sace a harin.

Shugaban ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar Neja cewa Gwamnatin Nijeriya za ta bayar da dukkan tallafin da ya dace wajen aikin ceto, agaji da ƙarfafa tsaro, yana mai jaddada cewa ta’addanci ba zai karya gwiwar Nijeriya wajen kare rayuka da al’ummominta ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata