Home Kasashen Ketare Trump ya cire Amirka daga WHO

Trump ya cire Amirka daga WHO

71
0

Shugaban ƙasar Amirka Donald Trump ya raba gari da hukumar lafiya ta duniya WHO, a daidai lokacin da cutar coronavirus ke ƙara mamaye Nahiyar Latin Amerika.

Tun da farko dai, Trump ya sanar da dakatar gudunmuwar kuɗin da ƙasar sa ke ba WHO a watan da ya gabata, inda yake zargin hukumar da rashin yin abun da ya dace wajen daƙile cutar tun a farkon lokaci.

Saidai a ranar Juma’a ya sanar da ficewar Amirka daga hukumar, wanda hakan ya kasance babban giɓi ga WHO kasancewar ƙasar babbar mai taimaka mata, inda ko a bara ta ba hukumar Dala miliyan 400.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply