A karshe Donald Trump ya amince da cewa Joe Biden ne ya ci zaben da suka kara, amma dai ya ci gaba da ikirarinsa na cewa an “tafka magudi” a zaben.
Trump ya bayyana haka ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce Biden ya yi nasara ne saboda an yi magudi.
Tun a makon jiya ne dai Joe Biden ya yi nasara a zaben da aka gudanar a ranar 3 ga Nuwanban nan, sai dai har yanzu hukumar zaben kasar Amirka bata bayyana wanda ya yi nasara a hukumance ba.
