Home Kasashen Ketare Trump ya kamu da corona ana dab da zaben shugaban kasa

Trump ya kamu da corona ana dab da zaben shugaban kasa

107
0

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da uwargidansa sun kamu da cutar corona bayan da wata babbar hadimar shugaban Hope Hicks ta kamu da ita.

Rahotanni dai sun ce Donald Trump ya shafe tsawon lokaci su na tare da Hicks a wannan makon.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Donald Trump, ya ce shi da matarsa Melania sun killace kansu har sai sun warke.

Rahotanni sun ce sun kwashe tsawon lokaci tare, har tafiye-tafiyen yawon kyamfe suka yi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply